27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Hajjin bana: Wani alhaji malamin addini ya rasu a Saudiyya

LabaraiHajjin bana: Wani alhaji malamin addini ya rasu a Saudiyya

A yayin da alhazai ke shirin dawowa gida Najeriya, an ƙara samun rasuwar wani alhaji, malami kuma mamba a tawagar malamai ta hukumar jinɗaɗin alhazai ta ƙasa wato NAHCOM.

Alhajin ya fito daga jihar Gombe

Malamin addinin, Dr Abdulrahman Maigona daga jihar Gombe ya rasu ne jiya kamar yadda sanarwa daga shugabar watsa labarai ta hukumar jinɗaɗin mahajjata musulmai ta jihar Gombe,  Hajiya Hauwa Mohammad, ta nuna. Jaridar The Punch ta rahoto.

Maigona, ya rasu ne a masaukin sa dake a otal ɗin Namma Muwada bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Wani shaidar ganau ba jiyau ba ya tabbatar da cewa malamin alhajin sai da yayi kalmar Shahada kafin rasuwar sa. Tuni aka tafi da gawar sa zuwa masallacin Harami domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sanarwar na cewa:

Cikin yarda da ƙaddarar ubangiji, Allah ya yiwa Abdulrahman Umar Maigona rasuwa yau (Alhamis) a ƙasar Saudiyya bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Yahaya Inuwa ya naɗa shi mamba a hukumar kula da jinɗadin mahajjata musulmai ta jihar Gombe, sannan lakcara ne a fannin koyar da ilmin addinin musulunci a jami’ar jihar Gombe.

An bayyana adadin alhazan da suka rasu ƴan Najeriya a Saudiyya

Maigona shine mahajjaci na uku da ya rigamu gidan gaskiya a lokacin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi jihar Nasarawa, ta rasu a ranar 29 ga watan Yuni, bayan gajeruwar rashin lafiya inda aka binne ta a Makka, yayin da Hajiya Hasiya Aminu daga Zaria, jihar Kaduna ta rasu a ranar Arfah jim kaɗan bayan ta dawo filin Arfah.

Wata Mahajjaciya ta rasa ranta sa’o’i kadan bayan dawowarta daga Arfah

A wani labari na daban kuma wata mahajjaciya ta rasu jim kaɗan bayan dawowar ta daga filin Arfah.

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar Hasiya Aminu, wata ‘yar jihar Kaduna. Ta rasu ne tana tsaka da barci jim kadan bayan ta dawo daga dutsen Arafat, kamar yadda makwaftan da ke cikin tanti suka bayyana.

Shugaban aiyuka wanda ya kasance shugaban ma’aikatan lafiya na Najeriya, Dr Usman Galadima, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa ba a san musababin abinda ya yi sanadin mutuwar ta ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe