24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda muka rayu a hannun ƴan ta’adda tsawon kwana 100 a tsare -Mutanen da aka sako na harin jirgin Abj-Kd

LabaraiYadda muka rayu a hannun ƴan ta'adda tsawon kwana 100 a tsare -Mutanen da aka sako na harin jirgin Abj-Kd

Mutanen da aka sako waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya ritsa da su a ranar 28 ga watan Maris, sun bayyana yadda suka rayu tsawon kwana 100 a hannun ƴan ta’adda da suka ɗauke su.

Daily Trust ta rahoto cewa bayan sako mutum bakwai daga cikin su a ranar Asabar, akwai sauran mutum 44 ciki har da ƙananan yara da tsohuwa ƴar shekara 85 da suka rage a tsare.

Sun samu kulawa a hannun ƴan ta’addan

Da suke magana da wasu ƴan jarida a Kaduna, uku daga cikin waɗanda aka sako ɗin ranar Asabar sun bayyana cewa ƴan ta’addan sun kula da su inda har shanu shida suka yanka musu a tsawon zaman su a tsare na wata uku.

Muhammad Daiyabu, wanda tunda farko aka sako matar sa mai juna biyu, yayi watsi da rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta cewa sun sha cizon macizai inda ya bayyana su a matsayin ƙanzon kurege. Sai dai ya bayyana cewa sun kashe aƙalla macizai goma da kunamu biyu a wurin.

Waɗanda suka tsare mu sune suka kashe da yawa daga cikin macizan, labarin da ake yaɗawa cewa macizai sun cije mu ƙarya ne, domin ba wanda maciji ya sara. A cewar sa

Daiyabu wanda yayi magana a madadin sauran waɗanda aka sako ɗin ya tabbatar da cewa sauran mutanen dake a tsare na raye cikin ƙoshin lafiya.

Yayi ƙarin hasken cewa an harbi ɗaya daga cikin su bisa kuskure lokacin yaran ƴan ta’addan ke wasa da bindiga.

Alburushin ya ƙarci ɗaga daga cikin mu a cikin sa, amma mungode Allah bai shiga cikin ba. Waɗanda suka ɗauke mu sun damu sosai lokacin da lamarin ya auku sannan sun bamu haƙuri.

Ana yaɗa labaran ƙarya akan su

Ya koka kan yadda labaran ƙarya ke yawo a kafafen watsa labarai, waɗanda yace ba z su haifar da ɗa mai ido ba ga sauran dake a tsare.

A cewar sa:

Bayan an sako ni, naji labarai waɗanda ba gaskiya bane. Zama a tsare ba abinda zaka yiwa ko maƙiyinka fata bane. Muna zuwa suka kwance bayan sun kama mu, sun cigaba da nanata mana cewa matsalar su ba tsakanin mu da su bane, amma da gwamnati ne.

Sun kula damu, ba su buge mu ba, cutar da mu ko tsangwama mana a tsawon kwana 100 da na shafe a can, sun yanka mana shanu 6 domin mu ci, idan bamu da lafiya, suna iyakar ƙokarin su wurin samo mana magunguna, sannan abinda ba zan taɓa mantawa da shi ba shine abinda suka yi na sako matata mai ɗauke da juna biyu. Hakan ya nuna cewa suna da tausayi a zuciyar su.

Ya roƙi gwamnati da ta cika musu buƙatun su domin a sako sauran mutanen dake tsare, inda yake cewa:

Babban abin damuwar shine halin da sauran mutanen da aka baro ke ciki a daji.

Yan ta’adda sun sako wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Ƴan ta’adda waɗanda suka kai hari a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sako wasu daga cikin fasinjojin da su ka ɗauke a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Ƴan ta’addan sun tayar da bam a wani ɓangare na jirgin wanda hakan yayi sanadiyyar tsayawar jirgin, inda bayan nan su ka buɗe wa fasinjojin jirgin wuta, inda su ka halaka mutum 62 ciki har da yara da tsofaffi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe