23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Msosi, mutumin da ya lamushe naman akuya guda, shinkafa 2kg da Donut 40 cikin mintoci 20

LabaraiMsosi, mutumin da ya lamushe naman akuya guda, shinkafa 2kg da Donut 40 cikin mintoci 20

Wani dan kasar Tanzania ya samu nasarar cinye shinkafa kilogram biyu da kuma naman akuya guda daya duk a lokaci daya, hakan yasa matarsa ta tsere ta bar shi saboda ganin mugun cinshi yayi yawa, Legit.ng ta ruwaito.

Saidi Msosi ya ci gasar cin abinci ta Tonga nyama a Morogoro kuma hakan ya bai wa mutane da dama sun yi mamakin yadda ya iya cinye donot guda 40 cikin mintoci 20.

A wata tattaunawa da Millard Ayo yayi da shi, Msosi ya ce sai da ya kai wa likita ziyara inda aka sanar dashi cewa girman cikinsa ya yi yawa ba kamar na sauran mutane ba.

A cewarsa:

“Na cinye donot guda 40 cikin mintoci 20. Sai da na fara cinye shinkafa faranti uku cikin hudu a hankali ina ci gaba da cin sauran a hankali,” a cewarsa.

Matarsa ta tsere

Ganin yadda yake cin abinci kamar gara ya sanya matarsa ta tsere zuwa tsauni mafi kusa, kuma ta gaji da girke-girke.

A gidansa yana cikin shinkafa kilogram uku da kuma kaza guda daya a lokaci guda a ko wacce rana.

“Ni gauro ne, ina hayar ‘yan mata don su yi min girki in biya su kudi. A yanzu dai ni gauro ne, kuma ba na bukatar mata,” a cewar Msosi.

A yanzu dai yana iya cinye shinkafa kilogram 10 da kuma naman akuya guda daya.

Msosi ya lashe gasa da dama

Msosi ya lashe gasar cin abinci wanda da kudin ya siya fili ya kuma gina gida. Yanzu haka yana da babura biyu duk ta dalilin gasar da yake shiga.

Msosi mai nauyin kilogram 72 ya musanta batun cin gasar ta hanyar amfani da tsafi.

Yadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa

An ba wa wani da ake zargin barawon kebur ne kwanon taliya, yayin da ake mishi horo a yankin Agorogbene na karamar hukumar Sagbama dake jihar Bayelsa, LIB ta ruwaito.

An kama wanda ake zargin, Preye Ayase da abokin harkarsa, Ringo Tareladei dumu-dumu suna satar keburan wutar da ke sada Ogobiri da yankin Agorogbene cikin Sagbama a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu.

Sai dai, Oiseibai Seperegha Godsgift M, shugaban kungiyar matasan yankin (CYA) ya yi alawadai da barnatawa, sacewa gami da tarwatsa wayoyin wutan da ke sada yankunan biyu da hatsabiban suka yi.

A wata takarda da babban sakataran watsa labaran shi, Mr Ebis Okpeke ya bayyana wa manema labarai, na nuna yadda shugaban kungiyar ya nuna rashin jindadinsa bisa aukuwar lamarin ba tare da zato ba, inda ya yi kira ga matasan yankin da su bar irin wannan mummunar dabi’ar, saboda hakan zai zama sanadiyyar lalacewar rayuwarsu, ta hanyar kawo cikas ga cigabansu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe