Wata kotun kasar Saudiyya dake garin Jidda, ta yanke hukuncin saki ga wata mata, a sakamakon rashin saduwa da ita da mijinta baya iya yi.
Kotun ta sauwake wa matar ne, a sakamakon auren da tayi kimanin shekara biyu, amma har yanzu tana matsayin budurwa, saboda mijin nata ya kasa gusar mata da budurcin nata.

Lauyan matar mai suna Rubab Al-Maib, ya shaidawa kotun ta Jidda cewa, wadansu dalilai na cikin gida ne, suka sanya ta nemi a raba auren.
Kotu ta sauwake wa matar
A nata hukuncin, kotun ta sallami matar saboda gabatar da hujjoji wadanda suka tabbatar da kamawar mijin wajen kusantar matar tasa domin sabuwar aure.
A jawabin sa yayin yanke hukuncin, alkalin yace, shi aure a musulunci ana yin sa ne, domin samar da farin ciki ga juna, da kuma samar da ‘yaya.
Matsayin saduwa a rayuwar aure
A wani jawabin, alkalin ya kara da cewa, saduwa tana daga cikin ginshikan abubuwan aure, sabo da haka idan har za’a sami namijin da bazai iya gamsar da matar sa ta fuskar saduwar ba to wajibi ne a raba su , bayan an bashi damar neman magani kuma ya gaza samu.
Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood
Wani bidiyo ya fara yawa a shafukan sada zumuntar zamani wanda fitaccen furodusa, Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa ya dauki hankulan mutane da dama.
A bidiyon, wanda Tashar Tsakar Gida ta nuna, an ga tsohuwar jarumar tare da sauran jarumai sanye da hula ta kungiyar mawaka da jarumai ta 13 X 13, inda mai shaddan ya rubuta “Rahama Hassan is back” ma’ana “Rahama Hassan ta dawo”.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com