23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An yi ram da likitan da ya yiwa mai ciki fyade tana tsaka da nakuda

LabaraiAn yi ram da likitan da ya yiwa mai ciki fyade tana tsaka da nakuda

An kama wani likita da ake zarginsa da yiwa wata mata mai juna biyu fyade yayin yi mata aiki, sannan anyi imani da wata kila ya yiwa wasu mata biyun a wannan ranar, LIB ta ruwaito.


Anyi ram da Giovanni Quintella Bezerra mai shekaru 32 bisa zarginsa da laifin fyade bayan an dauki bidiyonsa a boye yana yiwa wata mata fyade ta baki bayan ya mata allurar bacci a asibitin Mulher na São João de Meriti, Rio de Janeiro.

An bukaci mijin matar da ya bar dakin, wanda daga bisani ya gano abin da ya faru da matarsa bayan ya gane fuskar likitan a talabijin bayan an kama sa.

“Ban taba ganin wani abu makamancin haka ba,” a cewar wakili Barbara Lomba, ‘dan sandan da ke da alhakin binciken lamarin.

Matar ta bayyana wa iyalinta yadda tayi zaton sambatu take a lokacin da ya yi mata fyaden.

An ruwaito yadda ma’akatan asibitin suka shiga cikin damuwa bisa yawan magungunan da Bezerra ke bawa marasa lafiyansa.
Likitan na amfani da allurar kashe zafi fiye da ka’ida har ta kai ga iyaye matan basa iya rike jinjirayensu bayan haihuwa.

Saboda haka ne ma’akatan asibitin suka aje kamara a boye don ganin abun da yake aikatawa.

Hankalinsu ya matukar tashi ganin yadda ya ke cin zarafin matar ta hanyar yi mata fyade.

An ruwaito yadda ya mata fyade kusan sau goma.

A cewar ma’aikatan asibitin da suka dauki bidiyon, likitan ya yi wa wasu biyu abu makamancin haka a ranar, ‘yan sanda na cigaba da bincike don gano ko suma sauran mata biyun sun fuskanci irin farmakin.

A tiyata ta biyu na ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, ma’aikatan sun ce Giovanni “ya sanya wa kansa budaddiyar rigar tiyata, wacce ke sakaya surarsa gami da tsayawa a wurin da ke kange kowa daga ganin jikin mara lafiya tun daga wuya.”

A yawancin tiyatar da ake yi na ciro ‘da, ba a yin allurar gusar da hankali gaba daya, amma duk matan da aka wa aiki da safiyar ranar sun ce basa cikin hayyacinsu yayin aikin.

A cewar daya daga cikin marasa lafiyan: “Abu daya da kawai zan iya tunawa shi ne muryarsa. Ya yi ta magana cikin laushin murya a kunne na, abun ya bani mamaki. Ya tambayi ko ina lafiya.”

Sauran mutane biyun da suka ce su ma marasa lafiyan Bezerra sun isa ofishin’yan sandan a Brazil tun lokacin da zargin ya bayyana.

“Giovanni ya tsaya wajen wuya da kan mara lafiyan, ya fara da lankwasa hannunsa na hagu, yana matsashi gaba da baya,” a cewar shedar, kamar yadda G1 Rio de Janeiro ya bayyana.

“Daga yadda yake matsi da hannunsa, yana nuna kamar yana rike da kan mara lafiyan zuwa kwankasonsa.”

Tuni aka mika likitan zuwa gidan yarin Benfica.

An saurari shari’ar likitan a ranar 12 ga watan Yuli. Inda ake tuhumarsa da laifin fyade gami da yanke masa hukuncin shekaru 8 zuwa 15 a gidan yarin Brazil.

Yadda ‘yar Najeriya ta sheka lahira bayan garzayawa gaban likita don kara girman mazaunanta

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna poshcupcake_1, cikin alhini ta bayyana yadda kawarta, Crystabel ta mutu bayan yunkurin kara girman mazaunanta da ta yi, Prewedding Nigeria ta ruwaito.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta tare da sanya hotunan mamaciyar:

“Ina son sanar da jama’a cewa wata kawara ta rasu a wannan asibitin da ke Jihar Legas, kwanaki kadan da su ka gabata bayan ta je a yi mata aiki.

“Ba wai ina shawartar kowa da ya ki zuwa a inganta masa surar jikinsa ba ne, ka yi idan kana so.

“Amma ina shawartarka da ka kiyaye zuwa wurin likitocin da ke ikirarin sun samu gogewa a kasar waje, su zo Najeriya su dinga halaka matasa.

“Bayan gama aikin, ta sanar da likitan yadda ya ke ta zubar da jini. Amma a haka ya ce babu komai zai tsaya.”

Ta ci gaba da kalubalantar iya aikinsa inda ta ce bai damu ba ko da kawarta ta bayyana masa cewa tana ta zubar da jini.

Ta ce abin ban takaicin shi ne yadda ta rasu ba tare da sanar da wani kowa a gidansu halin da ta ke ciki ba. Sai wasu kawayenta da su ka san ta yi aikin ne su ka bibiyeta daga nan aka ba su takarda cewa gawarta tana ma’adana gawa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe