24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Haka za ku cigaba da kwadago har ku mutu, Tinubu ga LP da PDP

LabaraiHaka za ku cigaba da kwadago har ku mutu, Tinubu ga LP da PDP

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta tsaida ranar 16 ga watan Yuni a matsayin ranar zaben gwamnan jihar Osun, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola na fatan dawowa madafun iko a karo na biyu, yayin da Ademola Adeleke na PDP ya ke sahun gaba a gasar fidda gwamnan jihar.
Jam’iyyar LP ta tsaida Lasun Yusuf a matsayin ‘dan takarar gwamnanta.

Sai dai, Tinubu ya ce da kamar wuya PDP da LP su kai labari indai APC na takarar.

Yayin jawabi a zagayen kamfen, ya siffanta PDP da LP a matsayin “jam’iyyun lemar kwado.”
Ya bukaci jama’ar jihar Osun da su duba gaba abin da zai faru da su a taba su zabi APC.

“Kada kuri’u yanzu yana hannunku. Ku zama masu lura. Ku kula. Baza kuyi haka a banza ba.

“Ku tuna da yaran ku sannan ku zabi wanda ya cancanta yadda gaba zata yi muku dadi. Ku fito da yawanku. Kada ku damu da PDP da sauran jam’iyyun lemar kwado – jam’iyyu irinsu Labour, zasu yi ta kwadago har su mutu gaba daya. Ubangiji bazai maisheku laburori ba.”

Kungiyar kwadago ta kasa ta ba Gwamnatin tarayya kwana 21 ta sasanta da ASUU da SSANU

Kungiyar kwadago ta tarayya (NLC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya akan kawo matsaya ga yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’in, ASUU, Kungiyar Ma’aikatan jami’o’i Marasa koyarwa, NASU, Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya, SSANU da ta Kungiyar Malaman Fasaha ta kasa, NAAT suke yi.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar samar da kwamitin da za ta zauna da su don kawo matsaya cikin kwanaki 21,The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana hakan ne ta wata takarda wacce shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba da babban Sakataren Kungiyar, Kwamared Emmanuel Ugboaja suka sanya hannu bayan kammala wani taro.

Kungiyar ta ce zata shirya wani taro na musamman da kwamitin ayyuka (CWC) na kungiyoyin don NLC ta san matakin gaba da za ta dauka.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe