24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Musulmi/musulmi: Kada wani malami ko fasto yace muku ga wanda zaku zaɓa -Keyamo

LabaraiMusulmi/musulmi: Kada wani malami ko fasto yace muku ga wanda zaku zaɓa -Keyamo

Festus Keyamo, ƙaramin ministan ƙwadago ya roƙi ƴan Najeriya da su kiyayi malaman addini masu cewa suyi la’akari da bambancin addini wurin yin zaɓe a shekarar 2023.

Hakan na zuwa ne bayan martanin wasu mutane ciki har da shugabannin kiritoci na jam’iyyar APC, na yin watsi da matakin da jam’iyyar ta ɗauka na sanya Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu. Waɗanda dukkanin su musulmai ne. Rahoton Channels Tv

Keyamo ya magantu

Ba wanda zai yaudare mu, a matsayin mu na ƴan Najeriya, malami ne ko fasto, mu zaɓi ko mu ƙi zaɓar wani bisa bambancin addini a tikitin takarar.

A fara muhawara kan abubuwan da Bola Tinubu yayi a matsayin sa na gwamnan jihar Legas ba wai kan maganar tikitin musulmi da musulmi ba.

Ya ƙara da cewa shugabanci mai kyau shine abinda ƴan Najeriya ke buƙata.

Ya yabawa ƴan takarar shugaban ƙasa na APC

Keyamo ya yaba da ƴan takarar shugaban ƙasa na APC a matsayin gwamnoni waɗanda suka yi nasara a jihohin su da hangen nesa wurin zaɓo waɗanda suka gaje su.

Haƙiƙa, APC ta zo da mutum biyu waɗanda suka samu gagarumar nasara a jihohin su a lokacin mulkin su, sannan suka zaɓo waɗanda suka gaje su (Fashola da Zulum) da kuma tsohuwar matar gwamna kuma sanata a yanzu. Lamari ne na sayi ɗaya ka samu uku kyauta.

A cewar sa

Dalilin da yasa ban zaɓi kirista a matsayin mataimaki ba -Tinubu

A wani labarin kuma Tinubu ya bayar da dalilin da ya sa bai zaɓi kirista a matsayin mataimaki ba.

Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kare zaɓin sa na Kashim Shettima a matsayin mataimakin sa.

Kafin bayyana Shettima, lamura sun yi zafi kan batun tikitin musulmi da musulmi.

Yayin da ƙungiyar kiristoci ta Najeriya ke adawa da hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun buƙaci ƴan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta ba son zuciya ba.

Ya ce ya tuntubi mutane da dama game da batun mataimakin kuma ya godewa manyan mambobin jam’iyyar da abokansa na siyasa da manyan kasa “wadanda ke yi wa Najeriya kallo irin nasa.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe