24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Wani mutum ya halaka tsohuwa ƴar shekara 71, ya sayar da sassan jikin ta kan N22,200

LabaraiWani mutum ya halaka tsohuwa ƴar shekara 71, ya sayar da sassan jikin ta kan N22,200

Hukumar ƴan sanda a jihar Ogun, ta cafke wani mai suna Dauda Bello, mai shekaru 54, bisa zargin halaka wata tsohuwa Mrs Mesesi Adisa, mai shekaru 71 a duniya.

Dauda kuma ya yanke wuyan hannaye da idon guiwoyin matar sannan ya sayar da su ga wani akan kuɗi N22,200. Ƴan sanda sun shaida cewa wanda ya siya sassan jikin ya arce. Jaridar The Nation ta rahoto.

Ya shiga hannun hukuma

An dai cafke wanda ake zargin ne a ranar 7 ga watan Yuni, 2022 bayan ɓatan Mrs Adisa kwanaki kaɗan bayan ta bar gida.

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fada a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ƴan’uwan tsohuwar sun shigar da rahoton ɓacewar mutum a ofishin ƴan sanda na Sabo-Ilupeju.

Wanda ake zargin na safarar ƙananan yara tare da tsohuwar


Oyeyemi yace wanda ake zargin ya amsa cewa ya san matar, inda yace su dukan su suna harƙallar safarar ƙananan yara.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya gayyaci matar zuwa gidan sa a ranar domin tattauna harƙallar su, sai dai bayan zuwan ta ya fahimci cewa kamar akwai kuɗi masu yawa a tattare da ita.

Hakan ya sanya ya bugawa matar ƙaton icce a kai, wanda hakan ya sanya matar ta suma inda daga nan ya ɗauke ta zuwa cikin daji inda ya ƙarasa halaka ta.

Ya kuma ƙara bayyana cewa, lokacin da ya duba jikin matar, ya gano cewa matar na da N22,200 kacal ne kawai a tattare da ita, waɗanda ya ɗauke cikin takaici.

Bayan ya fahimci cewa buƙatar sa ta samun kuɗi daga wurin tsohuwar ba tayi nasara ba, sai ya yanke shawarar yanke wuyan hannayen da idon guiwoyin ta, waɗanda ya siyar ga wani mutum wanda yanzu haka ya arce.

Wanda ake zargin kuma ya kai jami’an ƴan sanda cikin dajin inda ya binne tsohuwar cikin wani ƙaramin kabari. An ɗauko ragowar jikin matar sannan an ajiye a wurin adana gawa.

A cewar Oyeyemi

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona su ka jefa gawar maigidan su a rijiya bayan sun halaka shi a Abuja

A labarin kuma wasu ma’aikata gidan gona sun halaka maigidan su sannan suka kefar gawar sa cikin rijiya a Abuja.

Yan sanda a Abuja sun bayyana yadda ma’aikatan gidan gonan wani manomi, Hussaini Aliyu Takuma, su ka halaka shi sannan su ka jefa gawar sa cikin wata rijiya kusa gonar sa a ƙauyen Jeida, cikin ƙaramar hukumar Kuje, a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa manomin ya ɓace ne a gonar sa a ranar 2 ga watan Yuni, 2022, sai dai bayan gudanar da kwakkwaran bincike an samu cewa kashe shi akayi sannan aka jefa gawar sa cikin rijiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe