23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yanzun nan: Dalilin da yasa ban zaɓi kirista a matsayin mataimaki ba -Tinubu

LabaraiYanzun nan: Dalilin da yasa ban zaɓi kirista a matsayin mataimaki ba -Tinubu

Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kare zaɓin sa na Kashim Shettima a matsayin mataimakin sa.

Kafin bayyana Shettima, lamura sun yi zafi kan batun tikitin musulmi da musulmi.

Yayin da ƙungiyar kiristoci ta Najeriya ke adawa da hakan, wasu masu ruwa da tsaki sun buƙaci ƴan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta ba son zuciya ba.

Ya ce ya tuntubi mutane da dama game da batun mataimakin kuma ya godewa manyan mambobin jam’iyyar da abokansa na siyasa da manyan kasa “wadanda ke yi wa Najeriya kallo irin nasa.”

Dalilan zaɓin Shettima a matsayin mataimaki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa da yake magana kan zaɓin Shettima a matsayin mataimaki, Tinubu yace gabaɗaya rayuwar sa, dukkan shawarwarin da yake yankewa game da tawagar sa da masu goyon bayan sa, suna akan turbar cancanta, gaskiya, basira, adalci, tausayi da kuma nagarta.

Ina ankare da maganganun da ake kan addinin wanda zai yi min mataimaki. Mutane masu daraja sun yi magana akan hakan. Wasu sun bani shawarar na zaɓi kirista domin na faranta ran kiristoci. Wasu sun ce na zaɓi musulmi domin na faranta ran musulmai. Gaskiya itace, ba zan iya yin duka biyun ba.

Kowanne ɓangaren mahawarar nada dalilai masu kyau masu goyon bayan matsayar su. Kowanne yana a daidai akan hanyar su. Dukkanin su ba su akan daidai akan abinda Najeriya ke buƙata a yanzu. A matsayin shugaban ƙasa, ina fatan na mulki ƙasar nan zuwa samun cigaba. Hakan zai ɓuƙaci sabon abu. Zai buƙaci ɗaukar matakai da baa taɓa dauka ba a baya. Kuma yana buƙatar hukuncin da a siyasance, suna da ƙaranci da matuƙar wahala.

Idan zan zama irin wannan shugaban ƙasar, dole na zama irin wannan ɗan takarar. Bari na ɗauki wannan matakin basirar mai tsauri ba domin siyasa ba sai domin ciyar da ƙasar mu gaba da kamfen ɗin jam’iyyar mu zuwa nasarar da ta dace da mu samu.

Nan shine wurin da batun siyasa ya zo ƙarshe, sannan dole shugabanci na ƙwarai ya fara. Yau, na sanar da zaɓi na cikin alfahari saboda nayi shi ba a kan addini ko domin faranta ran wani ɓangare ko wanin sa ba.

Nayi wannan zaɓin saboda nayi amanna wannan shine mutumin da zai taimaka min wurin samar da ingantaccen shugabanci ga ƴan Najeriya, ba tare da duba da bambancin addinin su, ƙabilun su ko yankin su ba

Tinubu ya bayar da haƙuri kan waɗanda za suji haushin zaɓin da yayi

Ga waɗanda za suji haushin zaɓin da Tinubu yayi, sai yace:

Bari na faɗi muku hakan gaba ɗayan ku, musamman waɗanda za suji haushin zaɓi na bisa la’akari da bambancin addini. Ba zan taɓa iya watsi da ƙorafe-ƙorafen addini da bambancin ƙabilun mutanen mu ba. La’akari da su wani muhimmin abu ne na shugabanci nagari. Amma addini, ƙabilanci da yanki ba za su riƙa samar da alƙiblar mu a koda yaushe ba.

Tinubu ya zaɓi wanda zai yi masa mataimaki

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gama yanke zaɓin sa akan wanda zai yi masa mataimaki.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wata ingantacciyar majiya mai tushe a ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu wacce ta nemi a sakaya sunan ta, ta tabbatar da hakan ga kamfin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe