24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Malami ya bayyana wani muhimmin abu da Buhari zai yi kafin wa’adin gwamnatinsa a 2023

LabaraiMalami ya bayyana wani muhimmin abu da Buhari zai yi kafin wa'adin gwamnatinsa a 2023

Abubakar Malami, ministan shari’a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, ya bayyana cewa kafin kammaluwar wa’adin mulkin gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a shekara mai zuwa, martaba da ƙimar Najeriya zata dawo, inda zaman lafiya zai samu gindin zama.

Shugaba Buhari na aiki tukuru wurin ganin lamura sun daidaita a ƙasar nan

Malami ya ƙara da cewa shugaba Buhari na aiki tuƙuru wurin hana idonsa bacci domin tabbatar da komai ya koma kan hanya, ba domin miƙa mulki cikin ruwan sanyi ba kaɗai, har da tabbatar wa ƙalubalen tsaron da ya addabi ƙasar nan ya zama tarihi. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Malami ya yi wannan furucin ne yayin da yake taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar babbar Sallah (Eid-El-Adha) ta wannan shekarar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Ina son tabbatar muku da cewa gwamnatin shugaban ƙasa Buhari ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen cigaba da yin duk me yiwuwa wurin dawo da ingantaccen tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ina fatan Allah SWT zai amsa mana dukkanin addu’o’in mu na samun zaman lafiya mai ɗore wa a jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya, haka nan kuma da miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi a farkon shekara mai zuwa.

Kullum ina kwana da baƙin ciki da takaici kan mutanen da matsalar tsaro ta shafa -Buhari

A wani labarin kuma shugaba Buhari yace kullum yana kwana da takaici kan mutanen da matsalar tsaro ta shafa.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana baƙin cikin da yake fama da shi akan matsalolin tsaron da su ka addabi ƙasar nan. Jaridar The Nation ta rahoto

Shugaba Buhari, a wani jawabi da yayi wa ‘yan ƙasa wanda da aka watsa da safiyar yau domin tunawa da ranar dimokuraɗiyya, yace yana rayuwa kullum da baƙin ciki da takaici kan waɗanda ta’addanci ya ritsa da su.

Ranar dai ta bikin tunawa da zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga watan Yunin 1993 wanda marigayi Moshood Abiola, ya lashe amma gwamnatin soji ta janar Babangida ta soke.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe