23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Tinubu ya zaɓi wanda zai yi masa mataimaki

LabaraiTinubu ya zaɓi wanda zai yi masa mataimaki

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gama yanke zaɓin sa akan wanda zai yi masa mataimaki.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wata ingantacciyar majiya mai tushe a ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu wacce ta nemi a sakaya sunan ta, ta tabbatar da hakan ga kamfin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Tinubu zai faɗi sunan mataimakin sa a cikin makon nan

Majiyar ta ce Tinubu zai bayyana sunan wanda aka zaɓa a mataimakin ga ƴan Najeriya cikin makon nan.

Wanda aka zaɓa mataimakin ya kasance tsohon gwamna kuma sanata daga yankin arewa maso gabas na Najeriya.

Mutumin sannan kuma an haife shi a musulmi, wanda hakan ya tabbatar da abinda gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya faɗi ranar Asabar cewa Tinubu zai yi tikitin musulmi da musulmi. A cewar majiyar

An bayyana abubuwan da ya duba wajen zaɓo mataimakin na sa

Majiyar ta ƙara da cewa a wajen zaɓin mataimakin, Tinubu bai yi tunanin addini ba, sai dai cancanta, ƙwarewa da kuma kaifin hankalin ɗan takarar.

Shawarwarin da aka bayar wajen zaɓar mataimaki sun ginu ne akan ɗauko mutum wanda zai iya yin aiki tare da ɗan takarar shugaban ƙasan wurin kai Najeriya matakin gaba. A cewar majiyar

Tinubu ya shirya zuwa yawon sallah ga shugaba Buhari a Daura, jihar Katsina, ranar Lahadi inda zai masa bayani akan zaɓin sa na mataimaki.

Tun da farko dai Tinubu ya zaɓi Ibrahim Kabiru Masari a matsayin mataimaki na wucin gadi.

2023: Hotunan wayar hannu ta musamman da Tinubu zai raba sun jawo cece-kuce

A wani labari na daban hotunan wayar hannu ta musamman da Tinubu zai raba sun jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Hotunan wayar hannu ta musamman ɗauke da hoton ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed, tare da tambarin jam’iyyar sun karaɗe shafukan sada zumunta yayin da aka tunkari zaɓukan 2023.

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa ƴan Najeriya da dama sun sanya hotuna da bidiyon wayar a shafin Twitter

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe