23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Da yogot ya siye zuciyata, Zainab Yusuf, wacce ta hadu da mijinta a Twitter

LabaraiDa yogot ya siye zuciyata, Zainab Yusuf, wacce ta hadu da mijinta a Twitter

Zainab Yusuf da Rayyan Tilde a wata tattaunawa da shafin BBC Hausa yayi da su sun bayyana yadda aka yi su ka hadu a Twitter har abin ya kai ga aure.

Zainab asali ‘yar Kano ce yayin da Rayyan Tilde dan Jihar Bauchi ne. Rayyan ya shaida cewa ya fara yi mata magana amma bata amsa mishi ba.

Daga bisani akwai wani abokinsa, Sadiq Kurfi wanda shi ma ya san ta yayi masa iso gareta bayan ya je Kano.

A bangarenta, ta ce bayan ya yi mata magana sakamakon yadda mutane ke tura mata sako yasa bata duba nashi ba balle ta amsa har sai bayan Sadiq ya mata magana.

A zuwansa na farko ya kai mata Yogot wanda hakan ya yi matukar burgeta kuma washegarin ranar ne ranar zagayowar haihuwarta inda ya kara kai mata wata kyautar.

Rayyan ya ce kasancewar karamar kyauta yayi mata amma ta shiga farin ciki kwarai, hakan ya ba shi kwarin guiwa inda ya ji ta shiga ransa.

Ita kuma a bangarenta, ta ce da yogot din da ya kawo mata ya siye zuciyarta don tana son yogot sosai.

Yayin da aka tambayeta idan bayan ya kawo mata kyautar zagoyowar ranar haihuwarta ne su ka fara soyayya, cewa Zainab tayi:

“Eh gaskiya tun farko ma da yazo din, yogot din da ya kawo min ya siye zuciyata. Kuma da yadda ya gabatar min da kansa.”

Ta bayyana cewa ta kula da wallafe-wallafensa na Twitter akan addini yake yi sannan ko gyara zai yi wa mutum cikin mutunci yake yi ba cin fuska ba.

Ga bidiyon tattaunawar tasu da BBC Hausa:

A karshe dai jaruma Mercy Aigbe ta karbi musulunci bayan aure da mijinta musulmi babu dadewa

Jaruman masana’ntar finafinai na kudancin Najeriya, sun hadu da sauran masoya jaruma Mercy Aigbe, inda suke tofa albarkacin bakin su akan rungumar addinin sabon biloniyan mijin nata da tayi, wato Kazeem Adeoti. 

Sharhin mutane akan wallafar da jaruma Mercy Aigbe din tayi

Mutane da yawa sun yi sharhi akan sakon Jarumar wanda ta wallafa a shafin ta na instagram a yanar gizo, wanda a ciki take tunkaho da sabuwar shigar da ta bayyana a ciki domin martani ga masu kushe ta. 

Kyakkyawar Jarumar wacce uwa ce ga yara biyu, ta nuna farin cikin ta da yanayin da take ciki a yanzu, da kuma matakin da take da burin shiga akan sana’ar ta a nan gaba. 

Mercy Aigbe din, ta wallafa bidiyo a karshen sati, a shafin ta na instagram wanda a ciki take nuna jin dadin shigar da tayi a matsayin ta na musulma kuma matar aure. 

Tayi alfahari da kasancewar ta mata agurin musulmi

Jarumar, wadda shigar ta ta nuna cewa lallai ita matar wani mai riko da addinin musulunci ce, tace ta dauki aniyar zama cikakkiyar Hajiya da gaske, kamar yadda kalmar take nufi. 

Tace : “Bazan yi karya ba, amma tabbas ina jin dadin wannan shiga ta Hajiya, mai yiwuwa nima zan zama Hajiya ta gaske, abin yana yi min dadi sosai, koma dai menene Allah daya muke bautawa”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe