28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda na samu juna biyu na haihu ba tare da saduwa da wani namiji ba -Wata mata

LabaraiYadda na samu juna biyu na haihu ba tare da saduwa da wani namiji ba -Wata mata

Wata mata ƴar ƙasar Ghana mai suna Aba, tayi iƙirarin cewa ta samu juna biyu sannan ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.

Shekarar matar huɗu rabon da ta sadu da wani namiji


Da take magana a wata hira da Barima Kaakyire Agyemang a tashar Step 1 TV, Aba tayi iƙirarin cewa bata sadu da wani namiji a tsawon shekaru huɗu da suka wuce.

A cewar ta, lokacin da ta fara jin wani baƙon ciwon ciki da kumburi, ta ɗauka cewa ‘fibroid’ (ƙarin mahaifa) ne.

Bayan taje asibiti, ta bayyana cewa likitoci sun shaida mata cewa tana bukatar ayi mata tiyata domin a cire shi.

Ta ƙara da cewa ta ji bukatar ta turo ƙarin mahaifar ɗin waje saboda hana yi mata tiyata a ciro shi, a mamakin ta, kawai sai jaririn yaro ya sulluɓo.

Tana buƙatar taimako wajen ɗaukar ɗawainiyar yaron

Matar wacce yanzu ta zama sabuwar uwa tana sayar da ruwa a bakin titi, ta kuma bayyana cewa bata da halin da zata ɗauki dawainiyar yaron. Ta kuma bayyyana cewa wata matar wani fasto ce take ɗaukar ɗawainiyar ta da ta jaririn kaɗan-kaɗan yadda zata iya.

Matar aure ta haihu a bandakin asibiti, ba ta taba sanin tana da juna biyu ba

A wani labarin na daban kuma, mun kawo muku yadda wata matar aure ta haihu a banɗakin asibiti, bata taɓa sanin tana ɗauke da juna biyu ba. Irin hakan na faruwa ga mace ɗaya a cikin mata 2,500 inda basu sanin suna ɗauke da juna biyu har sai sun haihu.

Wata matar aure bata taɓa sanin tana ɗauke da juna biyu ba har sai lokacin da ta ga hannun jaririn ta a cikin robar ɓandaki yayin da take ƙoƙarin ƙwarara ruwa bayan ta gama amfani da shi. Shafin LIB ya ruwaito

Lalene Malik, mai shekaru 23, ‘yan’uwan ta sun garzaya da ita zuwa asibitin A&E a Northwick Park Hospital, cikin Harrow, birnin Landan, bayan tayi ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki a gidan ta dake a Greenford, west London, ranar 26 ga watan Maris.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe