27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

ALAJABI : Bidiyon yadda wadansu maguna suka nunawa junan su Soyayya ta hayar hada taswirar alamar Soyayya 

LabaraiALAJABI : Bidiyon yadda wadansu maguna suka nunawa junan su Soyayya ta hayar hada taswirar alamar Soyayya 

A yanar gizo, muna ganin bidiyoyi na dabbobi masu kyau da burgewa, amma wannan bidiyon na wasu maguna, da suke nunawa junan su Soyayya ta wata bakuwar hanya, ya janyo hankalin mutane da daman gaske. 

Tasirin soyayya

Lallai Soyayya wani tasiri ne mai karfin gaske, wanda babu wata halitta da zata rayu cikin inganci ba tare da shi wannan kakkarfan tasirin na Soyayya ba. 

Wannan bidiyon na wadannan maguna, an dora shi ne a shafin tuwita na Buitengebieden, inda muka saba samo muku bidiyoyi masu nishadi.

Yadda haduwar wadannan masoya ta kasance

A cikin bidiyon an ga wadannan maguna wadda daya baka ce, daya kuma ruwan kasa, inda suka taho suka fuskanci juna da wani irin salo, tamkar ace yayin da saurayi ya hadu da budurwar sa. Sai kuma aka dan kalli nan da can aka dan basar, daga nan kuma aka dan matso kusa da juna aka dan saba da juna, sai kowannen su suka daga jelolin su suka, hada wannan taswirar, abin ban sha’awa. 

Mutane da dama sun yi sharhi akan wannan bidiyo mai abin ban mamaki da ban sha’awa.

Ga bidiyon anan

‘Yan sanda sun yi ram da matar da ta halaka mijinta bayan ta gano ya na soyayya da wata budurwa

Wata mata ta na hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumi da laifin halaka mijinta bayan ya bayyana soyayyarsa ga wata matar, kamar yadda ‘yan sandan Texas na Amurka su ka bayyana hakan, LIB ta ruwaito.

Yayin bayani a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, Harris County Sheriff, Ed Gonzalez ya bayyana yadda aka kama Carin Stewart mai shekary 51, wacce ta bayyana cewa da kanta ta halaka mijinta bayan sun yi hayaniya akan soyayyarsa da wata mata.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe