23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wata budurwa ta yashe dalibin saurayinta kakaf bayan ya yiwa iyayen sa karyar anyi garkuwa da shi ya karbi kudin fansar kansa daga gurin su

IlimiWata budurwa ta yashe dalibin saurayinta kakaf bayan ya yiwa iyayen sa karyar anyi garkuwa da shi ya karbi kudin fansar kansa daga gurin su

‘Yan sanda sun cafke wani matashi dan shekara 23, kuma dalibin wata makarantar kiwon lafiya mai suna Makindu, da ke kasar Kenya, a bisa tuhumar sa da shirya garkuwa da kansa, domin tatsar kudi daga gurin iyayen sa. 

A jawabin da ta fitar, a ranar Alhamis 7 ga wata , hukumar binciken manyan laifuka, DCI ta ce 

Yadda dalibin yayi karyar garkuwa da shi

Edwin Kamau, yayi layar zana tun ranar Lahadi da ta wuce, bayan ya katse lambar mahaifinsa, inda ya kira mahaifiyarsa yana shida mata cewa anyi garkuwa da shi. 

garkujwa
Wata budurwa ta yashe dalibin saurayinta kakaf bayan ya yiwa iyayen sa karyar anyi garkuwa da shi ya karbi kudin fansar kansa daga gurin su

Ya shaida mata cewa, masu garkuwa da shi suna bukatar a tura musu da kudin kasar Kenya shillings Sh70,000 wanda yayi daidai da N246,210.3, kafin itama ya katse mata waya”,. 

Kamar yadda rahoton ya fada

Iyayen sa sun kai rahoto ga yan sanda

” Cikin fusata da rudewa, sai iyayen nasa suka kai rahoton lamarin ga ofishin yan sanda, inda nan take suka shiga farautar masu garkuwar. “

Haka kuma, Kamau ya ci gaba da kiran mahaifan nasa yana yi musu barazanar cewa, yan garkuwar suna daf da kashe shi idan basu aiko da kudaden ba. 

A kokarin su na tseratar da rayuwar dansu, iyayen Kamau sun aika da shillings dubu goma 10,000 ranar Talata 7 ga wata, ta hanyar tsarin biyan kudi ta yanar gizo, yau kuma suka tura da shillings dubu arba’in 40,000. 

Yadda budurwar ta kwashe kudaden

Karbar kudin ke da wuya, sai Kamau din ya tafi gidan rawa, wato ( club) da dubu 10,000, domin ya sha giya tare da shagalin sa da wata karuwar sa da ya samu, wacce bai sani ba ashe itama barauniya ce, inda ta zuba masa kwaya a cikin lemon sha, kuma ta yi awun gaba da kudaden.

Bayan farfadowar sa a yau, shine ya kara kiran mahaifan nasa suka turo masa 40,000, wanda ya kwashe su ya zuba a cikin takalmin sa sau ciki. 

A yanzu haka, yan sanda sun kama shi, kuma yayi bayani, a yayin da ake bincikar sa cewa, kudin da aka bashi domin yin rajistar shiga zangon karatun gaba, sune ya kashe su, kuma bai san inda zai nemo su ba, shine ya sanya ya shirya wannan karya ta cewa an yi garkuwa da shi. 

Ya kara da cewa, anyi garkuwa ne da shi da wadansu abokan karatun sa, wadanda suma iyayen su suka biya shi kudin fansa. 

Jami’an tsaro, sun sami nasarar kwato sauran kudade kimanin Sh38,600, wadanda sukayi daidai da kudaden Najeriya Naira N135,767.394 daga gurin dalibin wanda yanzu haka yana ofishin yan sanda dake Koyole, inda yake jiran gurfana a gaban kotu.

Yau za a gurfanar da Amira Sufyan, budurwar da tayi karyar an yi garkuwa da ita gaban kotu

Ana sa ran rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja za su gurfanar da Amira Safiyan, gaban kotun majistare da ke Wuse a yau ranar 29 ga watan Yunin 2022 bisan yin karyar ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita.

A ranar 14 ga watan Yuni ne Amira ta bayyana a Twitter inda ta ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita da wasu mutane 16 ciki har da mata 3 masu juna biyu, LIB ta ruwaito.

Nan da nan mutane su ka razana bayan ta ce wadanda su ka yi garkuwa da su su na sanye da kayan ‘yan sanda ne sannan har gida su ka je su ja dauke su.

Bayan an gano inda take, ta bayyana a kafar taba bada hakuri inda tace da kanta ta je daji ta ki cin komai bisa ganganci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe