29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Yanzun nan: Dalilan da suka sanya na amince na zama mataimakin Peter Obi -Datti Baba-Ahmed

LabaraiYanzun nan: Dalilan da suka sanya na amince na zama mataimakin Peter Obi -Datti Baba-Ahmed

Datti Baba-Ahmed, mataimakin Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya bayyana dalilan da suka sanya ya amince yayi takara tare da tsohon gwamnan jihar Anambra.

Ya bayyana dalilan sa

Da yake magana bayan an bayyana shi a hukumance a birnin tarayya Abuja, Baba-Ahmed yace ya amince ya zama mataimakin Peter Obi saboda ya yarda da ƙwarewar sa wurin kai Najeriya matakin gaba. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya ƙara da cewa ya yarda da cewa Obi ba zai handami dukiyar ƙasar nan ba inda yayi nuni da cewa rawar da Obi ya taka a matsayin gwamnan Anambra ya tabbatar da hakan.

Darekta janar na yaƙin neman zaɓen Peter Obi, Dr Doyin Okupe, wanda shine mataimaki na wucin gadi ya sauka daga matsayin a ranar Alhamis.

Saukar sa nada nasaba da samar da mataimaki ɗan arewa domin samar da daidaito a tsakanin yankuna da kuma addini.

Datti Baba-Ahmed na da gogewa sosai

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed, mai shekaru 46 a duniya, gogagge ne a fannin ilmi, kasuwanci da siyasa.

Yayi ɗan majalisar tarayya a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007, sannan ya zama sanatan Kaduna ta arewa a shekarar 2011 a inuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC), inda ya shigar kuɗirori da dama cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

A shekarar 2011, Sanata Datti Baba-Ahmed ya kafa jami’ar Baze University, wata jami’ar kuɗi dake a birnin tarayya Abuja, da jami’ar Baba-Ahmed, a Kano (wacce ke jiran lasisi)

Na tsine wa Peter Obi, ba zai ci zabe ba tunda makwado ne, ba ya taimako, Fasto Mbaka

A wani labari na daban kuma Fasto Mbaka yace Peter Obi ba zai ci zaɓe ba tunda makwado ne.

Fitaccen faston Katolika kuma darektan Adoration Ministry Enugu Nigeria (AMEN), Fr Mbaka ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya, Peter Obi, ba zai taba zama shugaban kasa ba.

Mbaka ya shawarci ‘yan Najeriya da su marawa Atiku baya inda yace ya mayar da hankali wurin neman shugabanci kwarai don haka su share Peter Obi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe