28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

2023: Hotunan wayar hannu ta musamman da Tinubu zai raba sun jawo cece-kuce

Labarai2023: Hotunan wayar hannu ta musamman da Tinubu zai raba sun jawo cece-kuce

Hotunan wayar hannu ta musamman ɗauke da hoton ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, tare da tambarin jam’iyyar sun karaɗe shafukan sada zumunta yayin da aka tunkari zaɓukan 2023.

An sanya hotunan wayar a shafukan sada zumunta

Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa ƴan Najeriya da dama sun sanya hotuna da bidiyon wayar a shafin Twitter.

Idan aka kunna wayar, hoton Tinubu ke fara miƙa gaisuwa ga mai amfani da ita, sannan sai wasu kalmomi su biyo baya masu cewa:

Dimokuraɗiyya tana akan turbar yin amanna cewa akwai yiwuwar yin abubuwa na musamman a tattare da talakawa.

Haka kuma wayar tana amfani da layuka guda biyu. Dabarar raba wayar hannu kafin zaɓe dai sabon abu ne a Najeriya inda a baya abinda ake rarrabawa masu zaɓe kayan abinci ne.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su kan wayoyin da Tinubu zai raba

Osaretin Victor Asemota ya rubuta:

Wannan abu ne mai matuƙar kyau! Tafi daɗewa kan abinci.

Dami Elebe ya rubuta:

Kaddara cewa wannan wayar ta kasa yin shekara ɗaya bayan zaɓe. Ko kuma dole ta sanya ka sayar da ita domin siyan abinci amma zaɓi Tinubu ba abin yi bane.

Tony Bonanza ya rubuta:

Tinubu zai raba wayoyi, Atiku zai raba shinkafa da wake amma Peter Obi zai raba maganin matsalolin Najeriya.

Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki

A wani labari na daban kuma, wasu majiyoti masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki. Ɗan takarar na shugaban ƙasa a jam’iyyar APC bai fitar da wanda zai ɗauka a matsayin mataimakin sa ba wanda hakan ya sanya ƴan Najeriya zaman jira.

Dukkanin wasu alamu sun gama nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, zaa ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa na ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Majiyoyi masu ƙarfi waɗanda ke da alaƙa da tarurrukan da ake yi kan lamarin fitar da mataimakin su ka shaidawa jaridar Vanguard a jiya Laraba.

Majiyoyin sun ce jam’iyyar APC za ta tsayar da musulmi da musulmi ne a zaɓen shugaban ƙasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe