24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Dirama: Maniyyacin Bakano da bai samu tafiya ba yayi aikin hajjinsa a sansanin alhazai dake jihar

LabaraiDirama: Maniyyacin Bakano da bai samu tafiya ba yayi aikin hajjinsa a sansanin alhazai dake jihar

Kano – An yi karamar dirama a Kano ranar Alhamis yayin da daya daga cikin maniyyatan aikin hajji wanda bai samu tafiya zuwa kasa mai tsarki ba ya fara aikin hajjinsa a sansanin alhazai dake Kano.
A sansanin Alhazan, Malam Jibrin Abdu daga Gezawa ya Zama abun kallo bayan an ganshi ya saka harami kuma yace ya fara aikin hajjjnsa a sansanin.

hajj camp
Dirama: Maniyyacin Bakano da bai samu tafiya ba yayi aikin hajjinsa a sansanin alhazai dake jihar


“Na fara aikina tunda muna da dukkan abubuwan bukata a nan kuma babu shakka zan dawo in karasa. Na san yadda ake yi, ba wannan bane karona na farko ba kuma ba zai zama na karshe ba,” yace.


Ya kara da cewa ya siyar da gonarsa ne saboda yaje aikin hajji amma wasu miyagun shugabannin suka hana, duk da ya dauka hakan a matsayin nufin Allah.
Baya ga Malam Abdu, wata mata Suwaiba Sani tare da wasu sun dinga zuba tsinuwa kan duk masu hannu a abinda suka fuskanta. Matar cike da fushi ta bayyana cewa ba za ta taba yafe wa duk masu hannu a hana ta tafiya hajjin ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kalla maniyyata 745 aka bari a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar Alhamis bayan jirgin karshe na maniyyata ya tashi wurin karfe 3:45 na yamma.
Sakataren hukumar jin dadin alhazai na jihar Kano, Muhammad Abba Danbatta, wanda shima bai samu tafiya ba tare da wasu daraktocin hukumar, ya dora laifin kan hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya wacce ta ki karban taimakon gaggawa daga kamfanin jiragen sama na Azman duk da kara kwanakin rufe daukar jiragen sama da gwamnatin Saudi tayi.

Wani mutumi dan asalin kasar Iraqi ya isa Saudiya bayan shafe watanni 11 yana tafiya a ƙafa domin sauke farali a hajjin bana

Wani dan kasar Iraqi, mai suna Adam Muhammad wanda ya isa birnin Makkah da kafarsa, inda kafin isar sa sai da ya ratsa kasashe 11, tare da kwashe kimanin watanni 11 yana tafiya domin isa kasa mai tsarkin don sauke farali a hajjin bana.
Adam Muhammad wanda ya dade yana mafarkin ganin yakai ziyara kasa mai tsarki da kafar sa, abun da mutane da dama suke ganin abu ne da kamar wuya kasancewarsa mazaunin kasar Burtaniya, bayan isar sa kasa mai tsarki, ya yi umrah, ya kuma shafe lokaci mai tsawo a Ka’aba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe