24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ke duniya: Yadda aka tafka fyaɗe ga yarinya mai watanni 13 kacal a duniya

LabaraiKe duniya: Yadda aka tafka fyaɗe ga yarinya mai watanni 13 kacal a duniya

Wata ƙaramar yarinya mai watanni 13 kacal a duniya ta faɗa rashin lafiya bayan anyi zargin an tafka mata fyaɗe a makaranta

Daga kai yarinyar makaranta sai aka tafka mata fyaɗe

An kai yarinyar makaranta ranar Litinin 4 ga watan Yuli, 2022. Sai dai lokacin da mahaifiyarta ta dawo domin ɗaukar ta bayan an tashi makaranta, tace ta lura da akwai kumburi da jini-jini a gaban yarinyar. Shafin LIB ya rahoto.

Tun daga wannan lokacin yarinyar ta faɗa rashin lafiya.

Sakamakon gwaji ya tabbatar da zargin da ake na anyi mata fyaɗe

Mahaifiyar yarinyar tace an yiwa yarinyar gwaji washegarin ranar da lamarin ya auku, inda sakamakon gwajin ya tabbatar da anyi mata fyaɗe.


Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa shugabar makarantar ta ƙi bata haɗin kai inda take zargin ta da shafawa makarantar kashin kaji.

Makarantar da ake zargin anyi wa yarinyar fyaɗe dai itace Lohims Academy, a Ojota, jihar Legas.

Ana ƙara samun yawaitar fyaɗe a ƙasar nan musamman akan ƙananan yara. Ƙananan yara maza da mata na fuskantar barazanar fƴaɗe a koda yaushe saboda yadda dokokin ƙasar nan ba suyi wani tanadin hukunci mai tsauri ba akan masu aikata fyaɗe.

A baya an sha yin kira ga hukumomi kan su zartar hukunci mai tsauri akan masu aikata mummunan aikin fƴaɗe.

Yadda mai wankin mota yayi min fyaɗe sannan ya ɗirka min ciki -Yarinya ‘yar shekara 11

A wani labari na daban kuma, wata ƙaramar yarinya ta bayyana yadda mai wankin mota yayi mata fƴaɗe sannan ya ɗirka mata ciki.

Wata yarinya ‘yar shekara 11 ta shaida wa kotun sauraron masu aikata laifukan fyaɗe da cin zarafi ta Ikeja, jihar Legas, yadda wani mai wankin mota Ezekiel Udoh, mai shekara 39, yayi mata fyade sannan ya ɗirka mata ciki.

Jaridar The Punch ta samo cewa lamarin ya auku ne a yankin FESTAC Town, na jhar a shekarar 2020.

Jami’in ɗan sanda mai tuhuma, Z.A Dindi shine ya jagoranci yarinyar wurin bayar da shaidu.

Da take labartawa kotu yadda lamarin ya auku, yarinyar tace wanda ake zargin yayi amfani da ita har sau biyu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe