27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ali Ndume: Buhari ya sauke dukkan ministocinsa idan har yana son Najeriya da alheri

LabaraiAli Ndume: Buhari ya sauke dukkan ministocinsa idan har yana son Najeriya da alheri
  • Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, yace Buhari ya sauke ministocinsa matsawar yana yi wa Najeriya fatan alheri
  • A cewar Ndume, wanda dama shine shugaban kwamitin majalisa na harkar sojoji, yace tabbas Buhari mutumin kirki ne, amma na zagaye da shi ne matsalar
  • Ya koka a kan yadda aka aiwatar da kasafin 2020 amma mutanen arewa maso gabas basu samu wasu kayan tagomashi ba saboda mugayen wakilai

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkar sojoji, Mohammed Ndume yace shugaba Muhammadu Buhari ya sauya dukkan ministocinsa da sauran jiga-jigai da ya nada, matsawar yana yi wa ‘yan Najeriya fatan alheri a 2021.

Duk da Ndume ya ce Buhari mutumin kirki ne, amma yana zagaye ne da wadanda basa fatan ganin cigaban Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sanata Ndume ya fadi hakan ne jiya, yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

KU KARANTA: Dan sandan Najeriya da yaki karbar cin hancin naira miliyan 864 ya yi murabus

Sanata Ali Ndume | Photo Credit: The Guardian NG
Sanata Ali Ndume | Photo Credit: The Guardian NG

Ya koka a kan yadda wasu ministocin ba sa tattaunawa da mutanen jihohinsu balle su san matsalolin da suke fuskanta.

Kamar yadda ya ce, “Nayi matukar farin ciki da kasafin 2020, wanda aka aiwatar da a kalla kaso 90 cikin 100. Kuma ba a taba aiwatar da hakan ba a tarihin Najeriya ko kuma wata gwamnati da ta shude.

“Sai dai, har yanzu akwai wuraren da basu samu komai ba, daga kasafin da akayi, musamman arewa maso gabas, saboda rashin samun wakilan siyasa nagari ” cewar Ndume.

A kan batun garkuwa da mutane da rashin tsaro da ke cigaba da hauhawa a kasar nan, musamman a arewa maso gabas, sanata Ndume ya ce wajibi ne a bai wa sojoji manyan makamai don kawo karshen Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda, duk da alkawarin da shugaba Buhari da shugabannin tsaro suka yi na kawo karshen ta’addanci a 2021.

KU KARANTA: Majalisar koli kan shari’ar Musulunci ta yabawa El-Rufai kan rushe otal din da aka so ayi bikin nuna tsiraici

A wani labari na daban, Jigon babbar jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Enugu, Ayogu Eze, ya bayyana cewa kwanan nan wasu gwamnoni guda biyu daga yankin kudu maso yammacin kasar nan za su bar jam’iyyar PDP su dawo jam’iyya mai mulki.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Eze, wanda ya taba fitowa takarar gwamnan jihar Enugu a jam’iyyar APC a shekarar 2019, ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da kyauta ga wasu ‘yan jam’iyyar a lokacin murnar sabuwar shekara a jihar ta Enugu.

Mun gano yadda jigon APC din ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC ce za ta karbi gwamnatin jihar nan gaba idan har ‘yan jam’iyyar suka hade kansu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe