24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda direban mota ya katso bayan gidansa inda ya shafawa jami’in kula da titin da ya je kama shi

LabaraiYadda direban mota ya katso bayan gidansa inda ya shafawa jami’in kula da titin da ya je kama shi

Wani bidiyo da yake yawo a yanar gizo ya bayyana yadda direban wata mota ya tube kayansa, yayi bayan gida a hannunsa sannan ya shafawa jami’in LASTMA wanda yayi yunkurin kama shi, LIB ta ruwaito.

Lamarin ya auku ne a Jihar Legas wanda ya janyo mutane su ka taru suna ganin ikon Allah.

Duk da dai ba a tabbatar da wanne bangare bane a cikin Jihar Legas, amma an ga yadda direban ya tube tsirara tare da tsugunnawa yana bayan gida a hannunsa.

Bayan kammala bayan gidan ne ya shafawa jami’in hukumar kula da dokokin titin Jihar Legas wanda cikin gaggawa ya sauka daga motar tasa.

Lamarin ya bai wa kowa mamaki akan yadda direban ya nuna rashin sanin darajar kansa don bai damu da tsiraicinsa ba.

Wasu kuma su na ganin jami’in zai iya daukar cuta sakamakon yadda direban ya shafa masa bayan gidan.

Takaddama ta barke tsakanin direban adaidaita da fasinjarsa, ya dinga tsala mata bulala

Wani rikici ya balle tsakanin mai Adaidaita sahu a Kano da fasinjojinsa wanda hakan har ta kai ga ya dinga tsala musu bulala kamar yadda Dala FM ta ruwaito.

Mai Adaidaitan mai suna Abba ya bayyanawa wakilin Dala Fm yadda komai ya wakana inda ya ce:

“Abinda ya faru na dauko su daga Calawa zuwa Sabon Titi, sun yi kokarin in kai su hanyar Dorayi ni kuma mikewa zan yi hanyar Ja’iz.

“Dama bamu yi yarjejeniya da su ba kawai Sabon Titi muka yi zan kawo su kuma sun san a inda ake tsayawa a sauke mutane.”

Ya bayyana cewa da su ka isa Sabon Titin ne su ka nemi yi masa rashin kunya har da masu zaginsa a cikin kananan.

Ya bayyana cewa kasancewar mata ne yaga rashin dacewar ya dake su da hannu, sai ya samu bulala ya shaudawa karamar cikinsu.

Ya bayyana cewa akwai wacce ta shake shi a cikinsu, kuma dama yana aiki da bulala, sai dabarar ladabtar da su ta zo masa, hakan yasa ya fito da bulalar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe