Fitaccen mawakin gambara na Najeriya, Eedris Abdulkareem ya bukaci addu’ar ‘yan Najeriya yayin da ake shirin yi masa dashen koda, Nigerian Pulse ta ruwaito.
A wata takarda wacce ya saki ta shafinsa na Instagram ranar Laraba, 6 ga watan Yulin 2022, mawakin ya nemi addu’ar ‘yan Najeriya a matsanancin yanayin da yake.
“Mawakin da ya samu shahara daga wakarsa ta “Nigeria Jaga Jaga” ya na neman addu’ar ‘yan Najeriya da masoyansa da ke fadin Najeriya a wannan yanayin da yake ciki,” kamar yadda wani bangare na takardar ya zo.
Ba a dade da gane cewa ya kamu da ciwon koda ba a wani fitaccen asibiti da ke Jihar Legas, yanzu haka ana kulawa da shi.
A takardar an samu bayanai akan yadda wani dan uwansa ya amince zai ba shi koda don a dasa masa.
“An sanya ranar da za ayi dashen kodar ta kasance karshen watan Yuli kuma tuni aka kammala duk wasu shirye-shirye da gwaje-gwaje akan wanda zai ba shi kyautar kodar,” kamar yadda aka shaida a takardar.
Ta cigaba da cewa:
“Don haka a maimakon ‘yan uwan Abdulkareem da kamfanin Lakreem Entertainment Inc., muna bukatar addu’a’inku da kuma fatan alkhairinku ga Eedris yayin da mu ke fuskantar wannan kalubale.
“Muna fatan Eedris zai samu waraka ya kuma dawo da sana’arsa ta waka kamar yadda yake yi a baya. Za mu ci gaba da sanar da ku duk wani bayani idan ya samu.
“Muna fatan Ubangiji ya albarkace ku tare da baku kariya. Amin. Hon. Myke Pam na Lakreem Entertainment.”
An yankewa mawakin Amurka, R. Kelly shekaru 30 a gidan yari akan lalata da kananun yara
An yankewa mawakin kasar Amurka, R. Kelly daurin shekaru 30 a gidan yari ranar Laraba akan amfani da damar daukakarsa wurin lalata da kananun yara maso son sa, Time.com ta ruwaito.
An yi ram da mawakin kuma marubucin wakar mai shekaru 55 a shekarar da ta gabata aka gurfanar da shi bayan wadanda su ka zarge shi sun yi tunanin an share batun su don su bakaken fata ne.
Alkalin wani yanki na Amurka, Ann Donnelly ya daure shi bayan samun shaidu daga wadanda yayi lalatar da su akan yadda lamarin ya bata musu rayuwa.
Daya daga cikin wacce yayi lalatar da shi cewa tayi yayin da ya kalmashe hannunsa ya saukar da idonsa kasa:
“Ka sanya ni yin abinda ya daga min hankali. Dama mutuwa nayi akan abinda nake fuskanta da kuma yadda ka sanya naji a jikina. Ka tuna yadda muka yi?”
Kelly be yi magana ba a kotun.
Sai dai duk da tarin zargin da ake yiwa Kelly masoyansa da dama su na ci gaba da siyan kaset din wakokinsa yayin da ake ci gaba da zarginsa da yin lalata da ‘yan mata masu kananun shekaru a shekarar 1990 da doriya, inda labarin ya ci gaba da yaduwa.
Eedris Turayo Abdulkareem Ajenifuja wanda aka fi sani da Eedris Abdulkareem fitaccen mawakin gambara ne na Najeriya.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com