Mu ne muka kai farmaki Gidan yarin Kuje-Martanin kungiyar ISWAP

  • Post author:
  • Reading time:3 mins read
Kuje prison after security breach
Mu ne muka kai farmaki Gidan yarin Kuje-Martanin kungiyar ISWAP

Kungiyar ISWAP ta fito ta bayyana cewa ita ke da alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje a Abuja.
In ba a manta ba a daren ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka kai hari gidan yarin tare da sakin fursunoni sama da 800 ciki har da wasu manyan mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.
Wani dan takaitaccen faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a daren Laraba ya nuna yadda suke kabbara tare da harbe-harbe da kona motoci.

Harin gidan yarin Kuje: Mutane 64 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun tsere – cewar Ministan tsaro

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa kimanin mutane 64 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da ke tsare a gidan gyaran hali na Kuje sun arce bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a daren jiya.

Mista Magashi ya bayyana hakan ne a yau Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ya yi zagayi a gidan yarin.
Da yake bayar da adadin wadanda suka bace,Magashi ya ce kimanin mutum 600 daga cikinsu ne su tsere yayin harin amma an samo mutum 300.
Ya ce: “An kai harin ne da misalin karfe 10:30 na dare. Sun zo da yawa inda suka samu shiga gidan yarin har suka saki wasu daga cikin fursunonin da muke neman su a yanzu.
Ba da jimawa ba, za mu bayyana ainihin adadin fursunonin da aka kama. Baya ga haka, muna kokarin ganin abin da za mu iya yi don ganin an dawo da duk wadanda suka tsere.
“Gidan yarin na dauke da fursunoni kusan 994 sannan sama da 600 sun tsere. An kama mutane da dama kuma an mayar da su gidan yari. Muna tsammanin zuwa nan da yamma, za a iya kara kama wasu a dawo da su.
“Yanzu haka komai ya lafa. Mutanen da suka aikata wannan aikin,mun yi imanin cewa suna cikin wata ƙungiya ta musamman ne.
“Wataƙila ‘yan Boko Haram ne saboda muna da adadin waɗanda ake zargi yan Boko Haram a tsare, kuma a halin yanzu ba bu ko ɗaya a cikinsu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi