23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Gwamnati ta kori alkalin da ya raba auren wani mutum, daga baya ya koma ya dirkawa matarsa ciki

LabaraiGwamnati ta kori alkalin da ya raba auren wani mutum, daga baya ya koma ya dirkawa matarsa ciki

Gwamnatin Jihar Legas ta kori alkalin wata kotu, Ishola Adeyemi, wanda ake zargin ya raba auren wani da ya kawo kara, Olayemi Ayeni kuma ya koma ya kwace matarsa, Premium Times ta ruwaito.

Lamarin ya bayyana ne bayan wani bidiyo ya bayyana a shafin Facebook din nishadantarwa na “Ogbongefrienda” a 2016 ya yi ta yawo.

Sai dai babu wanda ya fahimci bidiyon da kyau, wanda aka wallafa shekaru shuda su ka gabata a kafar sada zumunta, sai dai ya bazu sosai.

A bidiyon wanda ya yadu, Ayeni ya bayyana yadda Alkalin, Adeyemi, wanda ya ke zargin matarsa, Doyin Okububi, ta kwanta masa a rai ya raba aurensu kuma ya hana shi damar rike yaransa.

Bidiyon da ya yadu

A cewarsa ya fara fuskantar tashin hankali ne bayan matarsa ta dena daraja shi bayan ya bata Naira miliyan biyar ta ja jari.

Mai korafin ya ce matarsa ta kwashe kayanta ta bar gidansa sannan ta kama wani gida kusa da nashi.

A cewarsa:

“Na samu matsala da matata, ta kwashe kayanta ta bar gidana sannan ta kama wani gidan kusa da nawa. Na bata Naira miliyan biyar don ta ja jari ta bude wata makaranta mai suna Greatest Kiddies Foundation. Wannan sana’ar ta janyo min matsala wanda na kasa ci gaba da iya tankwasa ta.”

Ya zargi alkalin da yayi shari’a tsakaninsa da matarsa da tilasta saki tare da dirkawa matarsa ciki.

“Bayan nan da watanni goma, na yi tunanin aurenmu zai iya gyaruwa ta hanyar sasanci. Alkalin, Dr Ishola Azakiq ya yi gaggawar raba aurenmu sannan ya dirka mata ciki bayan watanni 3 da raba aurenmu,” a cewarsa.

A bidiyon, Ayrni ya zargi alkalin da tura masa ‘yan sanda don su kama shi su kuma tura shi gidan yarin Kirikiri da ke Jihar Legas.

Cikin radadi yake bayyana cewa yanzu haka cikinta ya kai tsufar watanni tara, kuma na alkalin ne.

“Abinda ya fi damuna shi ne hana ni damar ganin yarana da mutumin yayi. Dakyar nake samun damar ganin yarana su ma a harabar makarantar. Yanzu kuma yaran su na karkashin kulawarsa; ya ci gaba da kula da kasuwancin da na ba matar jari. Ya hanani damar ganawa da yarana sannan ya dirkawa matata ciki tare da tura ni gidan yari,” inji mutumin.

Ya ci gaba da cewa yana so yaransa su dawo karkashin kulawarsa don ba ya son su tashi cikin rashin tarbiyya. Yana da hakinsa kuma zai iya tura su makarantar kwana. Ya bukaci taimakon ‘yan Najeriya a cikin bidiyon don su kwatar masa hakkinsa.

Gwamnatin Jihar Legas ta dauki mataki

A wata takarda ta ranar Talata wacce gwamnatin Jihar Legas ta saki ta ce:

“Tsohon alkalin kotun ya yi amfani da ofishinsa wurin yin abinda bai dace ba tare da nuna rashin sanin makamar aiki dangane da mutumin da ya kawo karar matarsa. Ya kwace matar tare da yaransa daga wurinsa.”

Sakataren gwamnatin jihar na hukumar DSVA, Titilola Vivour-Adeniyi, ta saki takardar.

A cewarta, hukumar shari’ar Gwamnatin Jihar Legas ta yi bincike akan lamarin da ya auku ne tsakanin shekarar 2014 da 2015. Kuma abubuwan da ta gano ya sanya ta kori alkalin daga aiki.

Yadda alkali ya ki sauraron lauyan da ya bayyana gaban kotu da shigar bokaye

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ki sauraron wata kara wacce lauya mai kare hakkin bil’adama, Malcolm Omirhobo ya gabatar bayyan ya bayyana gaban kotu sanye da kayan bokaye, LIB ta ruwaito.

A ranar Alhamis din da ta gabata, Omirhobo ya bayyana gaban kotun kolin sanye da kayan bokaye.

Ya shafa wani farin abu wanda ya zagaye shi da idonsa daya, ya sanya sarkar kafa sannan ya daura wani jan kyalle a kwankwasonsa tare da sanya gashin dabba a kansa.

Omorhibo ya sanar da manema labarai cewa hakkinsa ne sanya duk kayan da ya sanya bayan ganin an bai wa masu hijabi damar sanya abinsu.

A ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, lauyan ya bayyana gaban alkali Tijjani Ringim sanye da sutturar wacce ta janyo cece-kuce daga sauran lauyoyi wadanda su ka ce bai dace a saurare shi ba.

An kusa dakatar da shi tun daga wurin shiga kotun saboda shigarsa amma sai da ya shiga tare da kalubalantar dalilin hana shi.

Karar da Omirhobo ta farko mai lamba FHC/L/CS/929/2022, ya maka kara ga gwamnatin tarayya da sauransu yayin da korafinsa na biyu mai lamba FHC/L/CS/1392/2021 ya yi akan sojojin Najeriya da wasu mutane biyu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe