28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Muhimman abubuwan sani dangane da Dr Muhammad Sanusi Barkindo

LabaraiMuhimman abubuwan sani dangane da Dr Muhammad Sanusi Barkindo

Sakatare janar na OPEC, Muhammad Sanusi Barkindo, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Talata yana da shekaru 63 a duniya.

Rasuwar Muhammad Sanusi Barkindo ta zo kwatsam

Jaridar The Punch ta rahoto cewa rasuwar sa ta zo sa’o’i kaɗan bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin jakadan Najeriya nagari a duniya, bayan ya karɓi baƙuncin sa a fadar sa dake Abuja.

Ga wasu muhimman abubuwan sani dangane da shi:

1. An haifi Muhammad Barkindo a ranar 20 ga watan Afrilu, 1959, a Yola, jihar Adamawa. Ya rasu a ranar 5 ga watan Yuli, 2022 yana da shekaru 63 a duniya.

2. Ya kammala digirin sa na farko a fannin siyasa a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a shekarar 1981.

3. Yayi karatun dufuloma a fannin arziƙin man fetur a jami’ar Oxford dake Ingila a shekarar 1988. Sannan yayi digirin digir a fannin kasuwanci a jami’ar Washinton ta ƙasar Amurka a shekarar 1991.

4. Daga watan Janairun 2009 zuwa watan Afrilun 2010, ya riƙe muƙamin babban darektan kamfanin mai na Najeriya wato NNPC.

5. Ya riƙe muƙamin wakilin Najeriya a kwamitin tattalin arziƙi na OPEC daga shekarar 1993 zuwa 2008.

6. Memba ne a ƙungiyar International Energy Forum, Riyadh, Saudi Arabia, wacce ke taimakawa wajen samar da haɗin kai da tattaunawa tsakanin ƙasashe masu arziƙin man fetur da kishiyoyin su.

7. Barkindo ya shafe shekaru 6 a matsayin sakatare janar na OPEC, inda ya zama mutum na huɗu da ya taɓa riƙe kujerar daga Najeriya.

Da ɗumin sa: Muhammad Sanusi Barkindo sakatare janar na OPEC ya rasu

A wani labarin kuma Muhammad Sanusi Barkindo, sakatare janar na ƙungiyar ƙasashe masu fitar da man fetur (OPEC), ya rasu

Babban sakataren ƙungiyar ƙasashen dake fitar da man fetur wato ‘Organisation of Petroleum Exporting Countries’ (OPEC) Muhammad Sanusi Barkindo, ya rasu. Ya rasu ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Talata. Jaridar The Punch ta rahoto

Manajan darektan kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari ya sanar da rasuwar sa da safiyar ranar Laraba. Ya bayyana rasuwar sa a matsayin wani babban rashi ga iyalansa, NNPC, Najeriya, ƙungiyar OPEC da duniya baki ɗaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe