Yadda MC Tagwaye da dan uwansa suka rikita ‘Yar sa akan sai ta gane waye mahaifin ta

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
06791bf3b0d3429d
Yadda MC Tagwaye da dan uwansa suka rikita ‘Yar sa akan sai ta gane waye mahaifin ta

Dan wasan barkwanci nan na Najeriya MC Tagwaye ya nishadantar da masoyansa da mabiyansa a shafukan sada zumunta inda ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram.
MC Tagwaye tare da ɗan’uwan haihuwar sa sun haɗa kai don yi wa ‘yarsa tsokana.

Sun sa ‘yar a tsakiya

A cikin faifan bidiyon dai an ga MCTagwaye da dan uwan haihuwar sa sun saka ‘yar sa a tsakiya akan ta banbance waye mahaifinta
‘Yar Ta kafe su da ido tana kallon sub inda ta cika da rudani.

Kada daga cikin martanin mutane

leerah tace:
Kai dis is not fair……Baby gaba daya ta rude…..zata zama irin to waye babana a cikin su.”

lady_henriet ta ce:
Haba ya kuke haka ne.”

roselinetasha ta ce:
Baku kyauta ba gaskiya Chai see as she dey look from one to the other. Irin to waye a babana cikin wadannan mutane 2 Kun yi sa’a ba ta fashe da kuka ba.”

officialmaryambooth ta ce:

Gaskia kudaina takurawa ‘yata.”

aysha_imy tace:
Wannan ba adalci bane ❤️.”

takalma_culture4us ya ce:
Ku tanadi paracetamol dan zaku haifar mata da ciwon kai.”

iggys_feet ya ce:

Why una de like this. Ko ni kaina kuna rudani balle kuma wannan yar gimbiya.”

Babbar matsalar Kannywood shi ne karancin ilimi a masana’antar, Aminu Sharif (Momo)

Fitaccen jarumin Kannywood kuma mai gabatar da shirye-shirye a tashar Arewa 24, Aminu Shariff wanda aka fi sani da Momo ya bayyana babbar matsalar da ta addabi masana’antar Kannywood da kuma hanyar maganceta.

A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da shi a shirin Daga Bakin Mai Ita, ya fara da gabatar da kansa inda yace sunansa Muhammad Al-Amin Aliyu Sharif, inda yace akwai masu yi masa lakabi da sunan Momo da ya fito da shi a cikin fim din Ukuba.

Ya ce an haife shi a Kano, ya yi karatu tun daga firamare har jami’a a Kano inda yayi karatu a jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi karamar Diploma, babbar Diploma sai kuma Digiri da sauran takardun ilimi.
Ya ce ya fara shigowa masana’antar ne a matsayin marubuci, sai ya fara shirya shirin sannan daga bisani ya tsinci kansa a matsayin jarumi.

Yayin da aka tambaye shi matsayin mutumin banza ko na arziki, wanne ya fi son fitowa a shirin fim, cewa yayi ko wanne matsayi aka ba shi in har zai isar da sako yana amsa.

A cewarsa, matukar zai burge masu kallo kuma ya nishadantar da su tare da isar da wani sako, tabbas zai tsaya tsayin daka wurin taka rawar da aka ba shi.

An tambaye shi idan yana fuskantar kalubale daga wurin abokan sana’arsa akan shirin tambayoyi da yake yi musu, cewa yayi ba ya fuskantar wanu kalubale.

Ya ce hasali ma duk wanda aka ga yana shakkar amsa tambayoyin wadanda yawanci akan sana’arsa, wanda ya daga sa ko kuma rayuwarsa to tabbas yana da lam’a.

Kuma ya ce ta yuwu yana tsoron yin karya ne kasancewar akwai wadanda su ke kallon shirin da su ka san shi a waje kuma idan yayi karya sun sani. Don haka in har dai yana da gaskiya bai dace ace sun yi shakka ba.

An tambaye shi hanyar magance matsalar kannywood inda yace:

“Babbar matsalar Kannywood shi ne ilimi, yaduwar ilimi a tsakanin ayyukan da ake gabatarwa da kuma wadanda su ke gabatar da ayyukan. Idan aka samu cikakken ilimin yadda za a gudanar da harkar, mutane za su san me ya kamata su yi, wanne irin sakwanni ya kamata a isar sannan kuma su waye ya cancanta su gabatar.
Wannan shi ne abinda ya ke damun mu ta hanyar ilimi babu irin nasarar da ba za a samu ba sannan za a dinga yin shirye-shiryen da mutane za su dinga bugun kirji su na alfahari dasu.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi