2023:Uba Sani ya zabi mataimakiyar El-Rufai,a matsayin abokiyar takarar sa a zabe mai gabatowa

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
Uba Sani and Dr Hadiza Sabuwa Balarabe
2023:Uba Sani ya zabi mataimakiyar El-Rufai,a matsayin abokiyar takarar sa a zabe mai gabatowa

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani, ya zabi mataimakiyar gwamna Nasir El-Rufai, Hadiza Balarabe, a matsayin mataimakiyarsa a zaben gwamna na Shekarar 2023.

Ta ki amincewa

Masu binciken sun ce da farko ta ki amincewa da tayin amma daga baya aka shawo kanta ta amince.
Mista Sani ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Kaduna bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga sassan jihar.

Ta bada gudunmuwa

A cikin wata sanarwa da ya bayyana wa manema labarai, Mista Sani ya ce Misis Balarabe ta bayar da gudunmawa sosai da kuma ci gaban da gwamnatin El-Rufai ta samu na samar da ababen more rayuwa da kuma ci gaban jama’a.
Dokta Hadiza ta nuna kwazon aiki, aiki a kan lokaci, sadaukarwa da kuma aiki wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na mataimakiyar gwamna wanda hakan ya kara mata daraja ga masu ruwa da tsaki a jihar.
“Don haka ina kira ga mutanen jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Balarabe da akayi a matsayin abokiyar takara ta.
“Ina kuma umurtar su da su fito domin kada kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.
“hadin kan da ku ka bamu a shekarar 2023 shi ne zai ba mu damar gina jihar Kaduna cikin lumana da wadata.

Tare, mun kuduri aniyar sanya jihar ta zama wata maudu’in shugabanci na gari,” in ji Mista Sani.

Kwankwaso ya bayyana abinda yankin Inyamurai yakamata su koya daga Tinubu

Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, ya bayyana zaɓen 2023 a matsayin wata babbar dama ga yankin inyamurai.

Yankin Inyamurai ne koma baya a siyasa
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala wani taron jam’iyyar a jihar Gombe, Kwankwaso yace yankin inyamurai sun iya kasuwanci kuma mutanen su nada hazaƙa, amma yakamata su koyi siyasa, saboda a ɓangaren siyasa sune koma baya. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Ya bayyana cewa yankin bai samu ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki ba a ƙarƙashin jam’iyyun APC da PDP, amma yana da dama a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.

Ya bayyana cewa waɗanda ke faɗin

Ko da abokina (Peter Obi) yana son amsar mataimakin shugaban ƙasa, wasu mutane daga yankin kudu maso gabas ba zasu amince ba, wannan ba dabara bace.

Kwankwaso yaba Inyamurai shawarar abinda za su koya daga Tinubu
Dangane da zaɓin sa kan wanda zai yi masa mataimaki, Kwankwaso sai ya kada baki yace:

Muna da mutane da dama daga kudancin Najeriya a NNPP da za mu iya zaɓo mataimakin shugaban ƙasa a ciki, ɗaya daga cikin su shine ɗan jam’iyyar Labour Party da kuke magana akai.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi