Wani dan kasar Mexico ya daura aure da kada cikin kayatarwa da ban sha’awa

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
temp 22
Wani dan kasar Mexico ya daura aure da kada cikin kayatarwa da ban sha’awa

Wani magajin gari a kasar Mexico ya auri wata kada sanye da rigar aure, inda ya sumbaceta a mastayin cikar sigar aure.
Yana daga cikin tsohuwar al’adar ƴan asalin ƙasar, wanda Victor Hugo Sosa ya jagoranta, kuma ya kudurin aniyar kawo wadata a ƙauyen San Pedro Huamelula a kudu maso yammacin Mexico.

Ana wa kadar lakabi da Gimbiya

Kadar mai shekaru bakwai ta kasace mutanen garin na yi mata lakabi da ‘yar karamar Gimbiya, inda suke kallon ta a matsayin wata abar girmamawa mai wakiltar uwa ta duniya; Auren da shugaban wannan gari yana nuna haɗewar mutane da wannan dabba madaukakiya.

Bikin anyi shagali

Bikin ya kayatar da kade-kade da wake-wake, da raye-rayen gargajiya yayin da aka umurci ango da ya sumbaci sabuwar amaryarsa.
An yi ta kade-kade da ganguna a lokacin da mai unguwa ya dauki amaryar sa a hannunsa suna kewaye yayin da maza ke ta musu fifita da hulunan su.

An daure kadar dan gudun cizo

An daure bakin kadar don gudun kar ta ciji ango a lokacin da zai sumbace ta,inda ya sumbace ta sau ba adadi.

Kyakkyawar baturiya ta iso Najeriya wurin saurayin ta, tana shirin yin wuff da shi

A ranar Asabar 2 ga watan Yuli, 2022 da misalin ƙarfe ɗaya na rana, wata baturiya ‘yar ƙasar Canada, Natasha, za tayi wuff da wani angon ta ɗan Najeriya mai suna Gift.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa baturiyar wacce ta haifi yaro ɗaya ta shigo Najeriya a cikin ‘yan kwanakinnan domin haɗuwa da masoyin na ta a karon farko wanda suka haɗu a shafin Instagram shekara ɗaya da ta gabata.

An nuna bidiyon lokacin da baturiyar ta shigo Najeriya
Masoyan biyu sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da baturiyar ta iso Najeriya yadda suka rungume juna cikin shaukin ƙauna.

Haka ma wani bidiyo da aka wallafa a TikTok ya nuna yadda suka fara hira kimanin shekara ɗaya da ta wuce.

A cewar bidiyon, matashin ya tura mata saƙo a Instagram, inda daga gaisuwar mutunci abu ya riƙiɗe ya koma abota inda daganan suka tsunduma cikin kogin soyayya.

Duk da sukar da tasha daga wurin masu amfani da yanar gizo kan cewa Gift kawai na amfani da ita ne domin samun katin zama ɗan ƙasar Canada, baturiyar ta cigaba da kare soyayyar dake a tsakanin su ta hanyar wallafa bidiyoyi masu kyau.

Natasha lokaci bayan lokaci tana sanya bidiyon yaron ta manhajar TikTok. Sai dai abinda baa sani ba shine ta taɓa aure ko bata taɓa aure ba.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su
I_am_Mbuyi ya rubuta:

Dukkanin ku matasa ne masu jini a jika, kuna da damar da za kuyi rayuwa mai kyau a tare idan har za ku iya tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa.

FilipeDaCosta83 ya rubuta:

Za suyi aure, su tafi Canada, sannan da zarar ya samu zama ɗan ƙasa, zai rabu da ita. Idan kana tantama jira nan da shekara biyar ka gani.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi