Kungiyar kare hakkin musulmai ta Bukaci da a dage Jarabawar NECO da za a yi Ranar Sallah

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
Gwamnan Kwara ya ce yana goyon bayan amfani da hijabi ga mata musulmai a jihar
Kungiyar kare hakkin musulmai ta Bukaci da a dage Jarabawar NECO da za a yi Ranar Sallah

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO da ta sauya ranar jarrabawar da za a yi a ranar Asabar 9 ga watan Yuli shekarar, 2022, sakamakon ranar ta fado ranar farkon sallah
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan roko ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata sanarwa.

Shugaban kungiyar ya yi jawabi

Hukumar NECO ta sanya daya daga cikin jarrabawar ta mai suna Data Processing (Practical) a ranar Asabar 9 ga watan Yuli daga karfe 10.00 na safe zuwa 1.00 na rana,wanda wannan ranar ta ci karo da ranar farko ta ranar Sallah.
“Duba jadawalin jarabawar NECO 2022 (2022 NECO June/July SSCE Time-Table Examination Time-Table (27th June – 12th August, 2022) | Original Version.Muna da cikakkiyar masaniyar cewa ba da gangan aka saka wannan ranar ba domin a zahiri NECO ta bada hadin kanta ta hanyar bada hutu na tsawon mako guda don bikin Sallah (Litinin, 11 ga Yuli zuwa Juma’a 15 ga Yuli) kuma hakan ya bayyana a cikin jadawalin,”
in ji Akintola.

An bukaci NECO ta matsar da jarabawa

Ya ce, “Don haka muna kira ga mahukuntan NECO da su matsar da jarabawar wannan rana kadai (Asabar 9 ga Yuli, 2022) zuwa gaba domin dalibai Musulmai su sami damar yin jarabawar.
“Jarabawar da za a yi ranar Sallah za a iya matsar da ita zuwa ranar Alhamis 14 ga Yuli, 2022 wadda tana daya daga cikin ranakun da NECO ta kebe domin hutun Sallah. MURIC na yi wa hukumomi da ma’aikatan NECO da ma daukacin ‘yan Najeriya fatan murnar Sallah.”

Dan Najeriyan da ya lashe gasar Alkur’ani ta duniya ya riga mu gidan gaskiya

Matashi Sadiq Abdullahi Umar, wanda ya wakilci Najeriya a gasar karatun Alkur’ani ta duniya a kasar waje, ya rasu, Aminiya ta ruwaito.

Aminiya ta samu damar zantawa da dan uwan mamacin, Muhammad Kabiru Makarfi, wanda ya tabbatar da batun rasuwar ta sa.

A cewarsa:

“Malam Sadiq ya riga mu gidan gaskiya ne a kasar Sudan bayan wata gajeriyar rashin lagiyar da yayi bayan kwana 26 da komawarsa daga Kano.”
Ya rasu ne yana da shekaru 26 da haihuwa yayin da ya bar mahaifiyarsa da kuma sauran ‘yan uwansa.

An yi jana’izarsa a can Sudan inda ya rasu bisa yadda addinin musulunci ya tanadar.
Kafin mutuwarsa, Sadiq ya lashe gasar karatun Alkur’ani wanda aka gudanar a kasar Kuwait da kuma Kasar Qatar.
Shi ne wanda ya lashe gasar musanakar da aka yi a watan Maris din shekarar 2022 a Kasar Zanzibar.

Har ila yau, marigayin ya samar da kafofi da dama na koyar da karatun Alkur’ani a yanar gizo da kuma tashar YouTube.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi