Na so ace ana kai ziyara lahira, Matashin da budurwarsa ta rasu ana gab da aurensu

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Na so ace ana kai ziyara lahira, Matashin da budurwarsa ta rasu ana gab da aurensu
Na so ace ana kai ziyara lahira, Matashin da budurwarsa ta rasu ana gab da aurensu

Abdulmuhyi Bagel Garba, kanin kwamishinan wutar lantarki da kimiyya da fasaha na Jihar Bauchi, Hon Garba Bagel, ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta mai taba zuciya bayan watanni 6 da rasuwar budurwarsa, LIB ta ruwaito.

LabarunHausa ta ruwaito yadda Hauwa Abdullahi Shehu, dalibar aji uku a jami’ar Jihar Bauchi, Gadau ta rasu sakamakon hadarin motar da ta yi ana saura wata daya ayi aurensu.

Abdul, wanda dan sanda ne yana shirin auren Hauwa a Azare, Jihar Bauchi a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairun 2022, sai mutuwa tayi musu yankan kauna.

A ranar Asabar 2 ga watan Yuli, Abdulmuhyi yayi wata wallafa a shafinsa na Instagram inda yace:

“Naso ace ana zuwa lahira ziyara da na bukaci ganinki don sanar da ke yadda rayuwata ta kasance babu ke, Allah ya gafarta miki masoyiya.

“Amma watarana, radadin yana nunkuwa fiye da na ranar da lamarin ya faru. Allah ya sanya yi a Aljannar Firdaus.”

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah ya yi wa darektan fim din ‘Izzar So’ rasuwa

A yau ranar Lahadi ne muka tashi da labarin rasuwar darektan shirin fim dinnan mai dogon zango, Izzar so, Nura Mustapha Waye.

Kamar yadda jarumi Lawan Ahmad ya shaida a shafinsa na Instagram za an yi jana’izarsa ne karfe 11 na safiyar yau a Gidansa da ke Goron Dutse Primary School a Kano.

Ya kuma ci gaba da nema masa fatan gafara da kuma rahamar Ubangiji.

A dayen bangaren kuma, jarumi Ali Nuhu ma ya sanar da batun rasuwar tashi a shafinsa inda ya nuna cewa babu wani rashin lafiya da darektan yayi, kamar yadda ya wallafa:

“Innalillahi wa Inna ilayhi raji’un. Allah ya jarabce mu da babban rashi. Allah ya jikanka Nura ya kyautata makwancinka .

“Allah yasa annabi ya karbi bakuncinka. Jiya war haka muna tare ana raha. Allah ya jikanka da rahama.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi