Ondo: An yi ram da fasto da wasu bayan ceto yara 50 da aka boye su a coci

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Ondo: An yi ram da fasto da wasu bayan ceto yara 50 da aka boye su a coci
Ondo: An yi ram da fasto da wasu bayan ceto yara 50 da aka boye su a coci

Wani fasto da mambobin wata coci su na hannun hukuma bayan an gano inda yara 50 da aka yi garkuwa dasu a cocin da ke yankin Valentino a Jihar Ondo suke, LIB ta ruwaito.

An ceto yaran ne a daren Juma’a, ranar 1 ga watan Yuli.

A bidiyon da aka samu a yanar gizo anga yaran a motar sintirin ‘yan sanda kafin a wuce da su ofishin ‘yan sanda.

Yaran sun kai 50 kuma ana zargin an yi garkuwa da su.

Kungiyar matasa ta Ekimogun a wata takarda wacce shugabanta, Mr Famakinwa Lucaskakaki, ya ce an samu nasarar ceto yaran ne da taimakon jami’an Amotekun.

Kamar yadda takarda tazo:

“Da misalin karfe 2 na ranar Juma’a, 1 ga watan Yulin 2022, na samu labarin yadda a wata coci ta Valentino, garin Ondo wacce ake kira ‘Cocin Ondo’ ta rufe mutane a cikin cocin tsawon watanni 6, inda ake ce musu Jesus zai zo wurinsa a watan Satumban shekarar nan.

“Shugaban kungiyar kare hakkin Bil’adama da samar da adalci a gare su, Kwamared Omotayo Omolayo ya samu bayanin yadda komai ya auku, hakan yasa muka shirya mutane don su je duba mutane 50 da aka kulle.

“Cocin tana da dakuna infa faston ya kulle mambobin. An samu nasarar ceto su da taimakon ‘yan sanda, Jami’an Amotekun, Atariajanaku da kuma ‘yan sa kai wanda hakan ya janyo cece kuce har aka fara dukanmu.

“Daga faston har ma’aikatan cocin suna hannun ‘yan sanda kuma an wuce da su Akure.”

Ga bidiyon a kasa:

Yadda fasto ya yi layar zana da mambobin coci fiye da 20

Har yanzu dai ba a san inda Fasto Kalibala Samuel da mambobin cocinsa 20 su je ba kudan mako daya kenan, Legit.ng ta ruwaito.

Sai da Kalibala ya yi musu huduba mai ratsa jiki wacce ta sa su ka amince inda su ka rufe gidajensu su ka bi shi wani muri tare da kulle wayoyinsa.

Tuni ‘yan sandan yankin Mityana da ke kasar Uganda su ka bazama su na ta nemansu bayan batarsu inda ake fatan za a nemosu su dawo ga ‘yan uwansu.

An nemi wayoyinsu amma duk a kashe su ke kamar yadda ‘yan sandan su ka tabbatar. Kuma cikin mambobin gidaje bakwai da ya yi layar zanar da su akwai Namuwaya Jesca, Ssekyewa Shakim mai shekaru 19, Nampeewo Shifrah mai shekaru 17, Muteesasira Muhammad mai shekaru 10, Ssenabulya Muhammed mai shekaru 8, Nakintu Angel mai shekaru 4 da kuma Uwuzeeye Mable.

Bayanai sun nuna cewa sai da faston da mabiyan nasa sun rufe gidajensu ne sannan sun kashe wayoyinsu.

Kamar yadda takardar ‘yan sanda ta nuna, akwai mutum daya da ya samu yin magana da diyarsa wacce ba a riga an wuce da ita ba. Sai dai su na gama magana ta kashe wayarta ba tare da ya san inda ta ke ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi