28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kwankwaso ya bayyana abinda yankin Inyamurai yakamata su koya daga Tinubu

LabaraiKwankwaso ya bayyana abinda yankin Inyamurai yakamata su koya daga Tinubu

Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, ya bayyana zaɓen 2023 a matsayin wata babbar dama ga yankin inyamurai.

Yankin Inyamurai ne koma baya a siyasa

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala wani taron jam’iyyar a jihar Gombe, Kwankwaso yace yankin inyamurai sun iya kasuwanci kuma mutanen su nada hazaƙa, amma yakamata su koyi siyasa, saboda a ɓangaren siyasa sune koma baya. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Ya bayyana cewa yankin bai samu ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki ba a ƙarƙashin jam’iyyun APC da PDP, amma yana da dama a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.

Ya bayyana cewa waɗanda ke faɗin

Ko da abokina (Peter Obi) yana son amsar mataimakin shugaban ƙasa, wasu mutane daga yankin kudu maso gabas ba zasu amince ba, wannan ba dabara bace.

Kwankwaso yaba Inyamurai shawarar abinda za su koya daga Tinubu

Da yake bayar da misali da Bola Tinubu, yace dabara jagoran APC ɗin yayi wajen goyon bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, inda ya ƙara da cewa “yau shine ɗan takarar shugaban ƙasa a APC”

Kwankwaso yace babban zaɓin da yankin yake da shi shine ya haɗa kai da NNPP, “wannan babbar dama ce, idan suka rasa ta, zai zama babbar asara ce”

Dangane da zaɓin sa kan wanda zai yi masa mataimaki, Kwankwaso sai ya kada baki yace:

Muna da mutane da dama daga kudancin Najeriya a NNPP da za mu iya zaɓo mataimakin shugaban ƙasa a ciki, ɗaya daga cikin su shine ɗan jam’iyyar Labour Party da kuke magana akai.

Osinbajo na shan matsin lamba, akwai yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a NNPP

A wani labari na daban akwai yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a NNPP

Akwai sabbin shirye-shiryen da ake kitsawa a tsakanin ‘yan siyasan jam’iyya mai ksyan marmari wato New Nigeria Peoples Party (NNPP) da na hannun daman mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo domin dawo da shi cikin takarar shugaban ƙasa na 2023. Rahoton jaridar Vanguard.

Duk da cewa na kusa da mataimakin shugaban ƙasar sun bayyana hakan a matsayin jita-jita ce kawai, inda su ke cewa Osinbajo ba zai bar jam’iyyar APC ba, majiyoyi sun haƙiƙance cewa akwai magana mai ƙarfi kan duba yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe