23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Da duminsa: Allah ya yi wa kanin Sarkin daura rasuwa

LabaraiDa duminsa: Allah ya yi wa kanin Sarkin daura rasuwa
  • Allah yayi wa kanin sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, Abdullahi Umar rasuwa a ranar Lahadi
  • Ya rasu ne tare da abokansa 2 sakamakon hatsarin mota da suka yi a hanyar Katsina zuwa Daura
  • Marigayi Abdullahi ya mutu ya bar matarsa, yaransa 8 da kuma ‘yan uwansa, ciki har da sarkin

Allah yayi wa kanin Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar, Abdullahi Umar rasuwa, sakamakon mummunan hatsarin motar da yayi a hanyarsa ta Katsina zuwa Daura.

Marigayi Abdullahi da abokansa biyu ne hatsarin ya ritsa da su a ranar Lahadi, kamat yaddaa Vanguard ta wallafa.

Tuni dubbannin jama’a masu alfarma ciki har da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, suka fara kai wa sarkin Daura ta’aziyya a garin Daura.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An kwantar da Bola Tinubu a asibiti

Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota | Photo Credit: Vanguard
Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota | Photo Credit: Vanguard

Masari ya samu rakiyar Antoni janar, Barr. Ahmed El-Marzuq, Ambasada Adamu Sa’idu, mai bashi shawarwari a kan harkokin makarantun gaba da sakandare, Mal. Bashir Usman Ruwan-Godia da sauran hadimansa.

Gwamnan yayi wa mamacin fatan samun rahama, sannan yayi addu’ar Allah ya bai wa sarkin da iyalan mamacin hakurin jure rashinsa.

Marigayin ya mutu ya bar matarsa daya, yaransa 8 da kuma ‘yan uwansa, ciki har da sarkin Daura.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun yiwa Malami kisan gilla saboda ya kalubalanci garkuwa da mutane

A wani labari na daban, Shugaban tsohuwwar jam’iyyar R-APC, Alhaji Buba Galadimaa, ya bayyana cewa a tsarin yadda aka kafa jam’iyyar APC akwai yarjejeniya da aka yi kan yadda za ayi karba-karba tsakanin shugabannin jam’iyyar na Kudu dana Arewa kan wadanda za su mulki Najeriya.

Buba Galadima ya bayyanna hakane a wata hira da yayi da Daily Sun, wanda suka wallafa a ranar Asabar 2 ga watan Janairu.

A cewar shi: “Mutane hudu ne, biyu daga kudancin Najeriya, biyu kuma daga Arewacin Najeriya suka sanya hannu akan wannan yarjejeniya. Na san da wannan yarjejeniyar daga majiya mai karfi.

“Mutanen da suka zauna suka sanya hannu a wannan yarjejeniya, sun hada da tsofaffin gwamnoni guda biyu daga kudu maso yamma, da kuma wani gwamna mai ci a yanzu daga arewa, da kuma wani babban dan siyasa a arewa.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe