26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda ma’aikaci ya arce bayan kamfani yayi kuskuren biyan shi albashi har sau 330 a wata ɗaya

LabaraiYadda ma'aikaci ya arce bayan kamfani yayi kuskuren biyan shi albashi har sau 330 a wata ɗaya

Wani ma’aikacin wata masana’anta a ƙasar Chile ya tsere bayan kamfanin yayi kuskuren biyan shi albashin sa sau 330.

Mutumin wanda ma’aikacin kamfanin  Consorcio Industrial de Alimentos, an biya shi kimanin kuɗi £150,000 na aikin wata ɗaya, maimakon abinda yakamata a biya shi na £450 a matsayin albashin shi na watan Yuni. Shafin LIB ya rahoto.

Ma’aikacin ya gudu bayan karɓi kuɗin

Bayan ya karɓi kuɗin, maimakon ya mayar da aringizon da akayi masa ga kamfanin, sai ɗauki kuɗin ya ranta a na kare. Tun daga lokacin baa ƙara jin dukiyar sa ba.

Mutumin ya miƙa rahoton cewa an ciko masa kuɗin ga manajan sa, wanda shi kuma ya shaidawa waɗanda abin ya shafa

Da farko ya yarda zai dawo da kuɗin amma daga baya ya sauya shawara

Da farko, da aka ce masa ya dawo da kuɗin, ya yarda da zai yi hakan. Inda ya shaida musu cewa zaije banki washegari domin fara shirin dawo da kuɗaɗen. Amma bayan ya isa bankin, sai ya kwashe kuɗin yayi ɓatan dabo da su.

Kamfanin sun yi ƙoƙarin ji daga gare shi har na tsawon kwana uku amma abinda su ka samu kawai shine wani saƙo daga lauya cewa mutumin yayi murabus daga aikin sa.

Sun shigar da ƙorafi a wurin hukumomi, inda suke tuhumar mutumin da almundahana da sama da faɗin kuɗi, sai dai baa samu cafke shi ba tunda baa ganshi ba haryanzu.

Ana biyan ma’aikata £450 a wata a matsayin ƙarancin albashin a ƙasar Chile.

Sabon ma’aikacin gidan burodi ya sace N350,000, ya tsere a jihar Legas

A wani labari na daban kuma, wani sabon ma’aiƙacin gidan burodi ya arce da kuɗaɗe a jihar Legas.

Wani ma’aikacin gidan burodin Tasty Loaf Bakery dake titin Ajelogo lamba 12 a unguwar Mile ta jihar Lagos, mai suna
John Emeka, ya sace Naira 350,000 mallakar gidan burodin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, anga wanda ake zargin a cikin talabijin sirri ta gidan burodin, yayin da yake tserewa da kudin, wanda aka ce cinikin ranar Larabar 16 ga watan Maris ne gabaki daya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe