28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

An yankewa mawakin Amurka, R. Kelly shekaru 30 a gidan yari akan lalata da kananun yara

LabaraiAn yankewa mawakin Amurka, R. Kelly shekaru 30 a gidan yari akan lalata da kananun yara

An yankewa mawakin kasar Amurka, R. Kelly daurin shekaru 30 a gidan yari ranar Laraba akan amfani da damar daukakarsa wurin lalata da kananun yara maso son sa, Time.com ta ruwaito.

An yi ram da mawakin kuma marubucin wakar mai shekaru 55 a shekarar da ta gabata aka gurfanar da shi bayan wadanda su ka zarge shi sun yi tunanin an share batun su don su bakaken fata ne.

Alkalin wani yanki na Amurka, Ann Donnelly ya daure shi bayan samun shaidu daga wadanda yayi lalatar da su akan yadda lamarin ya bata musu rayuwa.

Daya daga cikin wacce yayi lalatar da shi cewa tayi yayin da ya kalmashe hannunsa ya saukar da idonsa kasa:

“Ka sanya ni yin abinda ya daga min hankali. Dama mutuwa nayi akan abinda nake fuskanta da kuma yadda ka sanya naji a jikina. Ka tuna yadda muka yi?”

Kelly be yi magana ba a kotun.

Sai dai duk da tarin zargin da ake yiwa Kelly masoyansa da dama su na ci gaba da siyan kaset din wakokinsa yayin da ake ci gaba da zarginsa da yin lalata da ‘yan mata masu kananun shekaru a shekarar 1990 da doriya, inda labarin ya ci gaba da yaduwa.

Lauyan Kelly ya nemi a rage shekarun da aka yanke wa mawakin zuwa shekaru 10 a gidan yarin kasancewar ya wahala a yarintarsa, ya yi fama da talauci, cutarwa sannan an dinga lalata da shi.

Lauyan ya ci gaba da cewa:

“Yanzu haka da ya girma, mutanen da ya yarda da su da dama sun ci gaba da damfararsa da kudi, kuma duk da ya biya su don su ba shi kariya.”

Tun shekarar 1990 da doriya aka fara zarginsa da lalatar inda a shekarat 1997 wata mata ta zarge shi da cutar da ita ta hanyar lalata da tozarta ta, daga baya kuma aka zarge shi da daukar bidiyon tsiraicin wata yarinya a Chicago, a shekarar 2008 wanda aka kammala shari’ar.

Kotun tarayya ta Brooklyn ta daure shi ne bayan ji daga bakin manajojinsa da hadu ansa akan yadda yake haduwa da yara mata kuma ya tilasta su yi masa biyayya, wanda a cewar alkalin ta’addanci ne.

Masu zargin nashi sun bayyana yadda yayi lalatar dasu tun kafin su kai shekaru 18 da haihuwa.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun ce sun yarda da cewa zai yada bidiyoyin tsiraicinsu da ya dauka idan har su ka fallasa shi.

Kamar yadda su ka bayyana, Kelly bai bayyana cewa yana da cutukan da ake samu ta hanyar saduwa ba, kuma ya nemi wani yaro ya taya shi lalata da wata yarinya da ke tsirara a garejinsa, kuma kamar yadda aka gani a bidiyon, har fitsari su ka yi a fuskar yarinyar akan karya dokokinsu.

Kelly ya ki amsa wani laifi. Amma lauyoyinsa sun ce duk wadanda yayi lalatar da su ‘yan matansa ne kuma bai taba tilasta musu yin lalatar ba, hasali ma sun ji dadin alakar.

Cikin shaidun da aka bayar har da na wata mawakiya Aaliyah wacce ya dirka mata ciki a shekarar 1994 lokacin tana da shekaru 15 da haihuwa. Shaidu sun nuna cewa sun yi aure ne bisa yin karyar cewa shekarun ta 18 a lokacin yana da shekaru 28.

Aaliyah ta yi aiki da Kelly a lokacin ta saki album dinta na “Age Ain’t Nothing But A Number. Ta rasu a shekarar 2001 sakamakon hadarin jirgin saman da tayi tana da shekaru 22.

Sai dai manema labaran ba su amince a lissafo sunayen wadanda ya lalata ba har sai dai idan su ne su ka bayyana.

An daure Kelly tun 2019 ba tare da an bayar da belinsa ba. Yanzu haka yana fuskantar laifin daukar bidiyon tsiraicin yara da kuma kawo cikas ga shari’a a Chicago kuma za a ci gaba da wannan shari’ar a ranar 15 ga watan Augusta.

Rashin chachanta ne yin wakar siyasa-cewar Mahmud Nagudu shahararen mawakin Kannywood

A wata hira da BBC ta yi da mawaki Mahmud Nagudu a cikin shirin nan mai suna Daga baki Mai ita,inda ya amsa tambayoyi da dama game da rayuwar sa.
Ga yadda hirarar ta kaya:


Meye asalin sunan ka?
“Ni suna na Ahmad Mahmud Abdulkadir an haifeni a Kano Unguwar Darma,na yi makarantar Allo dana Islamiyya,sannan nayi degree na a fannin Education.”


Tun kana shekara nawa ka fara waka?

“Na fara waka tun ina da shekaru goma sha daya.Wakan kannywood kuma na fara 1 ga wata Janairu 2002,daga nan ban sake waka ba sai shekarar 2005.”

A wani yanayi kafi rubuta waka?

“A gaskia bana rubuta waka,kawai sai dai in shiga in rera kuma cikin ikon Allah sai kaga waka ta fita.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe