23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Sauran sun tsufa: Tsoho mai shekara 87 ya siyo sabon akwatin saka gawar sa idan ya mutu

LabaraiSauran sun tsufa: Tsoho mai shekara 87 ya siyo sabon akwatin saka gawar sa idan ya mutu

Wani tsoho mai shekaru 87 a duniya, daga garin Busia cikin ƙasar Kemya, ya siyo sabon akwatin saka gawa domin biki binne shi nan gaba. Shafin LIB ya rahoto

Tsohon mai suna Aloise Otieng’ Ng’ombe, ya siyo akwatin a kimanin kuɗin ƙasar Ksh58,000 domin binne shi.

Tsohon ya daɗe yana siyo akwatunan da zaa binne shi

K2TV ta rahoto cewa Aloise ya siyo akwatunan saka gawar a shekarun 2009 da 2012. Tsohon mai ‘ya’ya 18 a duniya yace sabon akwatin wanda yanzu haka yana ajiye a shagon sa a yankin Obekei, zai zama shine akwatin da za’a sanya shi ciki nan gaba wajen binne shi idan ya mutu tunda waɗancan akwatunan da ya siya a baya sun zama tsohon yayi yanzu.

Yana son ya isar da muhimmin saƙo ga mutanen garin su

Ya kuma bayyana cewa siyo akwatin, zai isar da muhimman saƙo ga mutanen garin su.

Tsoho Aloise yace:

Ina son wannan ya zama darasi ga al’ummar yanki na. Za ka iya rasa abubuwan buƙata lokacin da kake raye.a da zarar ka mutu, mutanenza su yanka shanu, su siyo maka tufafi masu kyau da takalma bayan ka daɗe da tafiya barzahu. Hakan ya sanya na shirya bikin rakani wanda ya dace dani a cikin al’umma

Wani mutum ya haka kabarin sa ya sayo likkafani har da makara tsaf yana jiran mutuwa

A wani labari na daban kuma, wani mutum mai jiran mutuwar sa ya gina kabarin sa tare da siyo likkafani da makara.

Wani tsohon mutum dan shekara 70, wanda aka bayyana a matsayin Leonardis, ya bayyana dalilin da ya sanya shi haka kabarin sa, ya siyo akwatin gawar sa, da kuma sayo kayan shaye-shayen da za’a yi a bikin binne shi, duk da cewa a yanzu yana raye. 

Leonardis din yana da matan aure guda tara, amma uku daga cin su kadai ya yarda da su, basa cin amanar sa. 

Da yake magana da kafar Afrimax English, tsohon ya bayyana dalilin sa na yanke shawarar ginawa kan sa kabari, duk da cewa hakan bakon abu ne. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe