24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yau za a gurfanar da Amira Sufyan, budurwar da tayi karyar an yi garkuwa da ita gaban kotu

LabaraiYau za a gurfanar da Amira Sufyan, budurwar da tayi karyar an yi garkuwa da ita gaban kotu

Ana sa ran rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja za su gurfanar da Amira Safiyan, gaban kotun majistare da ke Wuse a yau ranar 29 ga watan Yunin 2022 bisan yin karyar ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita.

A ranar 14 ga watan Yuni ne Amira ta bayyana a Twitter inda ta ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita da wasu mutane 16 ciki har da mata 3 masu juna biyu, LIB ta ruwaito.

Nan da nan mutane su ka razana bayan ta ce wadanda su ka yi garkuwa da su su na sanye da kayan ‘yan sanda ne sannan har gida su ka je su ja dauke su.

Bayan an gano inda take, ta bayyana a kafar taba bada hakuri inda tace da kanta ta je daji ta ki cin komai bisa ganganci.

Kamar yadda ta wallafa:

“Don Allah duk mai lambata ta WhatsApp ya duba don na tura sakon inda nake. Bayan wasu masu garkuwa da mutane sanye da kayan ‘yan sanda sun zo har gida sun sace mu a bangarori daban-daban a Abuja. Mu 17 ne kuma a ciki akwai mata 3 masu juna biyu da kananun yara guda 2.”

‘Yan sanda za su tuhumi Amira akan yada labarin karya don rikita mutane a yau.

Shehu Sani ya ayyana wasu gaggan barayin daji da ‘yan garkuwa 4 wadanda tilas a hukunta su  idan har ana so ta’addanci ya kau

Shehu Sani wanda shine tsohon sanatan na yankin Kaduna ta tsakiya, a majalisar dattawa zagaye na takwas, ya ce ta’addanci da yake faruwa a halin yanzu, wanda yan ta’addan suke aikatawa a cikin daji, bazai zo karshe ba har sai an hukunta wadanda ya ambata, hukuncin da ya dace. 

Shehu Sani yayi bayani bayan an saki wasu mutane

Sanin ya bayyana hakan ne, bayan an saki mutane goma sha daya 11, da aka yi garkuwa da su a harin jirgin Abuja zuwa Kaduna. A sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa, yayi farin ciki da sakin su, amma akwai wadansu karin mutane da aka yi garkuwa da su a kan titin Zamfara zuwa Sokoto. 

Ya ayyana aikin baryin da jahilci

Ya bayyana cewa, wannan aiki na dakikanci da jahilci, da yake faruwa, yana faruwa ne saboda shugabannin yan ta’addan suna nan suna ta’asar su yadda suke so. 

Ya bayyana sunayen su kamar haka: Turji, Kachalla, Manjagara, da kuma Baleri. Ya nuna matukar yakinin cewa, idan har aka yi wani hukunci akan wadannan da ya ambata, to tabbas za’a sami saukin ta’addanci. Kadan daga cikin sakon nasa na tuwita, yana cewa,

“Matukar dai Turji, Kachalla, Manjagara da kuma Baleri, suna walwala, to babu Zancen ganin karshen ta’addanci “.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe