23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda alkali ya ki sauraron lauyan da ya bayyana gaban kotu da shigar bokaye

LabaraiYadda alkali ya ki sauraron lauyan da ya bayyana gaban kotu da shigar bokaye

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ki sauraron wata kara wacce lauya mai kare hakkin bil’adama, Malcolm Omirhobo ya gabatar bayyan ya bayyana gaban kotu sanye da kayan bokaye, LIB ta ruwaito.

A ranar Alhamis din da ta gabata, Omirhobo ya bayyana gaban kotun kolin sanye da kayan bokaye.

Ya shafa wani farin abu wanda ya zagaye shi da idonsa daya, ya sanya sarkar kafa sannan ya daura wani jan kyalle a kwankwasonsa tare da sanya gashin dabba a kansa.

Omorhibo ya sanar da manema labarai cewa hakkinsa ne sanya duk kayan da ya sanya bayan ganin an bai wa masu hijabi damar sanya abinsu.

A ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, lauyan ya bayyana gaban alkali Tijjani Ringim sanye da sutturar wacce ta janyo cece-kuce daga sauran lauyoyi wadanda su ka ce bai dace a saurare shi ba.

An kusa dakatar da shi tun daga wurin shiga kotun saboda shigarsa amma sai da ya shiga tare da kalubalantar dalilin hana shi.

Karar da Omirhobo ta farko mai lamba FHC/L/CS/929/2022, ya maka kara ga gwamnatin tarayya da sauransu yayin da korafinsa na biyu mai lamba FHC/L/CS/1392/2021 ya yi akan sojojin Najeriya da wasu mutane biyu.

An dakatar da shi bayan Omorhibo ya ce:

“Mai girma mai shari’a, dokokin ba su yi cikasa da kundin tsarin mulkin Najeriya ba.”

Bayan sauraron korafinsa, Alkali Ringim ya umarci Omirhobo ya yi wa kotu magana yadda za ta gane sannan ya nemi ya sauya shigarsa zuwa ranar da za a dawo a ci gaba da shari’ar.

Kamar yadda alkalin yace:

“Ba za ka iya bayyana gaban kotu a haka ba, hakan na nuna karancin gogewarka. Na dage karar nan kuma wajibi ne ka zo ka gabatar da kanka yadda ya dace a gaban kotu kuma kada ka sake bayyana a haka.”

Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Oktoban 2022.

Barr Khadijah: Kyakkyawar Lauya da take neman mijin aure ido rufe wanda za ta more dukiyar ta da shi

Wata zukekiyar lauya tayi wata wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wacce ta janyo maganganu kala-kala. Barr Khadijah ta bayyana yadda ta samu daukaka a rayuwarta amma duk da hakan take ganin rayuwa tana yi mata kunci tunda bata da miji, hakan yasa ta garzaya kafar sada zumuntar don bayyana kokon bararta watakila tayi dace.

Wannan wallafar ta ci karo da ta matan da suke ganin cewa in har mace tana samun isassun kudade, bata bukatar miji. Ta bayyana cewa kudi ba matsalarta bane, miji kadai take bukata.

Khadijah ta ce:

“Duk abinda ka mallaka a rayuwa, mutum na shiga cikin wani hali mutukar babu miji.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe