22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Mata ta ta gudu ta bar ni a asibiti ta dawo gari tana gayawa mutane na mutu – Inji wani mai gungulimi 

LabaraiMata ta ta gudu ta bar ni a asibiti ta dawo gari tana gayawa mutane na mutu - Inji wani mai gungulimi 

Wani mutum da aka bayyana sunan sa a matsayin Basirigara Theodomir, ya bayar da labarin yadda matar sa ta wulakantar da shi a asibiti, a lokacin da yake matukar bukatar ta a kusa da shi. 

Da yake magana da kafar Afrimax English, mutumin wanda yana da  ‘yaya har guda  bakwai, ya ce, matar tasa ta banzatar da shi ne bayan ya rasa hannayen sa da kafafu, ta inda a tunnanin ta babu ta yadda zai iya tabuka komai ga iyalan nasa. 

Yadda matsalar ta same shi

mata
Mata ta ta gudu ta bar ni a asibiti ta dawo gari tana gayawa mutane na mutu

Theodomir din, wanda mai gadi ne, yace a da can shima garau yake kamar kowa, dalilin wannan nakasa tasa shine wata rana ne yaje yawon gudun tsinka jini, yayi gudu kimanin kilomita uku, bayan ya dawo gida sai ya shiga bandaki domin yayi wanka. 

A fadar sa, yana zuba ruwa a jikin sa sai kafafuwan sa da hannayen sa suka sandare. Daga nan sai suka je asibiti da guraren masu magunguna, amma ba’a sami nasara ba. 

Matar sa so take ya mutu

Haka kuma ya shaida cewa, matar tasa tana so ne ya mutu, Saboda halayyar ta da gwada masa, inda ta gudu ta baro shi a asibiti, kuma ta dawo tana shaidawa mutane cewa wai ya mutu, duk da cewa suna da yaya har guda bakwai da ita. 

Mutumin wanda yayan nasa a halin yanzu sun girma, rake yake siyar wa, duk da yanayin da ya ke ciki, kuma wani abin sha’awar shine, ya sami wata matar wadda take kula dashi a yadda yake a hakan, duk da cewa ita ma tana fuskantar caccaka daga mutane.

Wani mutumi ya shekawa matar sa da ruwan zafi tana tsaka da bacci

Wani Isaac Ekeh, ya watsawa matar sa Stella ruwan zafi tana cikin barcin dare.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ba da rahoton cewa lamarin ya faru ne 31 ga watan Mayu da karfe uku na dare,lamarin dai ya farune a Satellite Town, Alakija Amuwo karamar hukumar Odofin jihar Lagas.

Ba suyi fada ba

Misis Ekeh, wata kwararriyar ilimi ce wace lamarin ya faru da ita, ta shaida wa NAN a wata hira da aka yi da ita a wayar tarho a ranar Litinin, ta bada labarin cewa sun ci abincin dare tare kafin afkuwar lamarin.


Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe