24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Osinbajo na shan matsin lamba, akwai yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a NNPP

LabaraiOsinbajo na shan matsin lamba, akwai yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a NNPP

Akwai sabbin shirye-shiryen da ake kitsawa a tsakanin ‘yan siyasan jam’iyya mai ksyan marmari wato New Nigeria Peoples Party (NNPP) da na hannun daman mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo domin dawo da shi cikin takarar shugaban ƙasa na 2023. Rahoton jaridar Vanguard.

Na hannun daman Osinbajo na cewa ba zai bar APC ba

Duk da cewa na kusa da mataimakin shugaban ƙasar sun bayyana hakan a matsayin jita-jita ce kawai, inda su ke cewa Osinbajo ba zai bar jam’iyyar APC ba, majiyoyi sun haƙiƙance cewa akwai magana mai ƙarfi kan duba yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan jihar Kano,Alhaji Rabiu Kwankwaso, shine ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, wata sabuwar jam’iyya mai tashe a jihohin arewacin ƙasar nan da dama.

Dalilan da su ka sanya ake duba yiwuwar takarar Osinbajo/Kwankwaso

Ɗaya daga cikin dalilan da su ka sanya ake maganar takarar Osinbajo/Kwankwaso, shine domin samar da shugabanci na daban wanda ‘yan Najeriya da dama ke muradi wanda Osinbajo ya zo da shi ga ‘yan Najeriya. A cewar ɗaya daga cikin majiyoyin.

A ɗaya ɓangaren kuma, Kwankwaso sanannen gogaggen ɗan siyasa ne a yankin arewa maso yamma, wanda cikin sauƙi zai sa Osinbajo ya kai labari.

Wannan sabon shirin, a cewar majiyoyin, wasu daga cikin na hannun daman Osinbajo ne tare da wasu manyan ‘yan siyasa na arewa ke kitsa shi.

A cewar majiyoyin, shirin shine a sauya Kwankwaso, wanda jam’iyya ta miƙa sunan shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, ta hanyar amfani da damar sauya sunan ‘yan takara wacce zaa bayar a cikin watan Agusta.

A cewar ɗaya daga cikin majiyoyin, lissafin da ake yi, shine addini zai taka muhimmiyar rawa kan wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari a 2023, sannan sanya Osinbajo, wanda kirista ne daga Kudancin Najeriya, zai tabbatar cewa arewa ta samar da mataimaki musulmi cikin sauƙi, a saboda haka Kwankwaso shine ya cancanta da zama mataimakin Osinbajo.

Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki

A wani labari na daban kuma, an bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki. Wasu majiyoyi masu ƙarfi ne su ka bayyan hakan.

Dukkanin wasu alamu sun gama nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, zaa ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa na ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Majiyoyi masu ƙarfi waɗanda ke da alaƙa da tarurrukan da ake yi kan lamarin fitar da mataimakin su ka shaidawa jaridar Vanguard a jiya Laraba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe