29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wasu da ban sani ba ne su ka sace min takardun makaranta, Tinubu ga INEC

LabaraiWasu da ban sani ba ne su ka sace min takardun makaranta, Tinubu ga INEC

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da Hukumar Zabe mai zaman kanta, INEC, cewa ya yi wata tafiya ne lokacin da wasu su ka sace masa takardun makarantarsa, Daily Trust ce ta ruwaito.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne yana cikin jiga-jigan National Democratic Coalation, NADECO da su ka fita wajen kasar nan lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

A takardar rantsuwar da yayi wacce ya hada da fom dinsa na takarar shugaban kasa, Tinubu ya ce ya yi wata tafiya ne a watan Oktoban shekarar 1994 zuwa Oktoban 1992, bayan dawowarsa ya tarar an sace takardunsa na makaranta.

Yayin da Tinubu ya bar bayani dangane da makarantar Firamare da Sakandaren da yayi a fom din INEC din, ya ce ya yi karatun digiri a Jami’ar Chicago tsakanin 1972 da 1976 inda ya karanta fannin tattali.

Ya kara da bayyana yadda yayi karatu a fannin kasuwanci inda yayi wata digirin.

Bayanin Tinubu ya ci karo da bayaninsa na baya musamman 1999 lokacin da ya lashe zaben gwamnan Jihar Legas.

Ya ce ya yi karatun firamare a St Paul Children School, Aroloya, sannan ya zarce Home School a Ibadan tsakanin 1958 da 1964; sai kuma yayi karatun sakandarensa a Kwalejin Gwamnati da ke Ibadan (GCI), tsakanin 1965 da 1968.

Bayan an yi caa akansa, tsohon gwamnan ya boye bayanan makarantar firamare da sakandarensa a 2003, lokacin da yayi takara.

Ya ce daga Ibadan ya zarce kwalejin Richard Daley da ke Chicago tsakanin 1969 da 1971.

Sai kuma ya ce ya yi karatu a karamar Jami’ar Chicago da kuma Jami’ar Chicago.

A takardun da ya gabatar, a lokacin wani fitaccen lauyan Najeriya, Marigayi Gani Fawehinmi, ya musanta bayanin inda yace akwai karya a ciki.

Har kotun koli sai da Fawehinmi ya kai lamarin amma aka yi fatali da karar saboda wasu dalilai.

Sai dai a fom din dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gabatar da digirin digir wacce ya kammala a 2021 a matsayin makurar takardarsa ta makaranta.

Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki

Dukkanin wasu alamu sun gama nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, zaa ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa na ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Majiyoyi masu ƙarfi waɗanda ke da alaƙa da tarurrukan da ake yi kan lamarin fitar da mataimakin su ka shaidawa jaridar Vanguard a jiya Laraba.

APC za ta tsayar da musulmi da musulmi takara

Majiyoyin sun ce jam’iyyar APC za ta tsayar da musulmi da musulmi ne a zaɓen shugaban ƙasa.

Da aka tambaye su dangane da damar da gwamnan jihar Filato yake da ita, wanda kirista ne, ɗaya daga cikin majiyoyin yace ‘wasu mutane ne kawai ke da wannan shawarar. Tinubu ba zai iya yin takara tare da Lalong ba.

Ya ƙara da cewa wasu na hannun daman Tinubu, sun yi amanna cewa Shettima, wanda yasan burin takarar Tinubu sosai da sosai shi yakamata ya samu kujerar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe