26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

‘Yan sanda sun cafke wani matashi bisa laifin yiwa tsohuwa ‘yar shekara 75 fyaɗe

Labarai'Yan sanda sun cafke wani matashi bisa laifin yiwa tsohuwa 'yar shekara 75 fyaɗe

‘Yan sanda a jihar Anambra a ranar Asabar sun cafke wani mutum mai shekara 30 a duniya bisa zargin yin fyaɗe ga wata tsohuwa mai shekaru 75 a duniya.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar a birnin Awka.

Yace wanda ake zargin, wanda ɗan asalin ƙauyen Eyiba ne a jihar Ebonyi, an cafke shine da misalin ƙarfe 4 na yamma ranar Juma’a a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.

An cafke shi lokacin da yake yiwa tsohuwar fyaɗe

Mr Ikenga, yace binciken farko ya nuna cewa an kama wanda ake zargin ne yayin da yake cikin aikata laifin a gonar matar a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.

Cafke wanda ake zargin ya biyo bayan neman agaji da tsohuwar tayi ne, hakan ya janyo hankalin mutanen dake wucewa da maƙwabta inda su ka garzaya zuwa wurin sannan su ka damƙe shi.

Ya sha dukan tsiya a hannun mutanen gari

Kafin a miƙa wanda ake zargin a hannun ‘yan sanda, sai da mutane su kayi masa ɗan karen duka, a cewar ‘yan sanda.

Kakakin hukumar ta ‘yan sanda yace an kai wanda ake zargin da tsohuwar da lamarin ya ritsa da ita zuwa asibiti domin duba lafiyar su.

An cafke tsoho mai shekaru 80 bisa laifin yin fyaɗe ga yarinya ‘yar shekara 11 a Borno

A wani labari na daban kuma, wani tsoho mai shekaru 80 ya shiga hannun ‘yan sanda bisa laifin aikata fƴaɗe ga yarinya ‘ƴar shekara 13 a duniya.

Jami’an ‘yan sandan jihar Borno sun cafke wani tsoho mai shekaru 80, Saleh Bukar, bisa laifin yin fyaɗe ga wata ƙaramar yarinya mai shekaru 11 a duniya.

Shafin LIB ya rahoto cewa, da yake tasa ƙeyar wanda ake zargin a gaban manema labarai ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, 2022, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar, yace yayar yarinyar ce mai suna Falmata Ali, ta lura da aukuwar lamarin bayan taga wani irin ruwa na fitowa a gaban yarinyar. A cewar ta daga baya yarinyar ta faɗi mata gaskiya inda tace Bukar yayi mata fyaɗe sau da dama a lokuta daban-daban.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe