24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Kotu ta daure wani Alkali bayan an gan shi sau 3 a shekara yana yawo tsirara

LabaraiKotu ta daure wani Alkali bayan an gan shi sau 3 a shekara yana yawo tsirara

Wata kotun koli da ke Ohio ta daure wani alkali tare da dakatar da shi bayan ganinsa a karo na uku cikin shekara daya yana tuka mota tsirara, LIB ta ruwaito.

Scott Blauvelt, mai shekaru 50 yana cikin manyan alkalan yankin tun shekarar 1997, inda aka dakatar da shi saboda ganin yadda yake yawo tsirara.

Tsakanin shekarar 2018 da 2021, an kama shi yana tuka mota tsirara har sau biyar, sau uku a cikin watanni 12 da su ka gabata.

A karon karshe kuma an ga yadda ya haske wata matashiyar mata wanda hakan yayi sanadiyyar kai shi gidan yari.

Dama tun a baya an kama shi da rashin kamun kai a bainar jama’a da kuma tukin ganganci a shekarar 2020, an tilasta masa yin wani shiri na shekaru biyu don horar da shi akan kamun kai, ta yuwu hirarwar bata yi aiki ba.

Yayin da ya amsa laifinsa a wannan makon, an daure shi kwana 14 a gidan yari sannan an dakatar da aikinsa tsawon shekaru 5.

Kotun kolin ta kara da cewa alamu suna nuna cewa Scott Blauvelt ya kamu da cutar tabin kwakwalwa kuma ya nuna nadamarsa akan abinda ya yi.

An sanar da shi cewa zai dawo ya ci gaba da shari’a matsawar an gano cewa ya warke gaba daya da cutar da ke damunsa.

A karon farko za a bawa Musulmi mukamin alkalin kotun koli a kasar Isra’ila

Musulman Larabawa suna da yawan kaso 21 cikin dari na yawan mutanen dake kasar Isra’ila, amma ba a taba zabar Musulmi ko daya ba a matsayin alkalin kotun koli ba tun da aka kafa kasar Isra’ila.

Musulmi daya da ya taba aiki a kotun kolin kasar shine Abdul Zuabi, wanda shi ma an bashi mukamin ne na rikon kwarya, wanda bai wuce shekara daya ba a shekarar 1999.

Sai dai a wannan karon sunayen alkalan da aka wallafa na kotun kolin ya canja salo bayan fitowar sunan alkalin gundumar Tel Aviv, Khaled Kabub, da mataimakin shugaban kotun, da kuma shugaban fannin tattalin arziki na kotun, ana ganin cewa Khaled Kabub yana daya daga cikin manyan ‘yan takarar.

Kwamitin da aka nada don zabar alkalan za ta fidda gwani daga cikin su a karshen watan Nuwamba, domin samun wanda zai maye gurbin Alkali Menachem Mazuz da Hanan Melcer, wanda suka yi murabus, sai kuma Mai Shari’a Karra da Neal Handel wanda za su yi murabus shekara mai zuwa.

Akwai yiwuwar Kabub zai maye gurbin Karra, wanda yake shine Balarabe daya tal dake aiki a kotun.

Kotun kolin dai ta sanya Larabawa a benci tun a shekarar 2003, lokacin da wani Balarabe Kirista, mai suna Salim Joubran, ya samu mukamin daya daga cikin kwamitin alkalan kotun kolin, inda hakan kokari ne na kawo karshen nuna bambanci a fannin shari’a na kasar Isra’ila, musamman ma a kotun koli.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe