23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Bidiyo: Yadda tsananin kishi ya sanya mijina ya cire min ido da ‘yan yatsu -Wata matar aure

LabaraiBidiyo: Yadda tsananin kishi ya sanya mijina ya cire min ido da 'yan yatsu -Wata matar aure

Wata mata mai suna Maureen Atieno Omolo, ta bayyana yadda mijinta ya cire mata ido, ya datse mata ‘yan yatsu sannan yaji mata raunika da adda da dama a jikinta.

Mijin ta na da tsananin kishi

Da take tuno mummunan lamarin a wata hira da Afrimax TV, matar tace niyyar mijinta a lokacin shine ya halaka ta a maimakon ya rasa ta ga wani namijin.

Omolo ta bayyana cewa su huɗu ne a gidan su, sannan ta zama marainiya tana da shekara 9 a duniya inda ta rasa dukkanin mahaifan ta. Ta zama marainiya tana da da ƙananan shekaru inda alhakin ɗaukar nauyin kan ta da na ƙannen ta ya dawo kan ta.

Dole ta sanya ta yin aure da wuri

A cewar dole ce ta sanya tayi aure tana da shekara 15, domin samun wanda zai taimaka mata kula da ƙannen ta. Duk da dai bata son yin aure da wuri, tayi tunanin cewa hakan shine kawai zaɓin da take da shi a wannan lokacin.

Ta ce mijin ta na fita aiki kullum domin samu abinda za su ci da kula da iyali. Sai dai akwai wani babban ƙalubale. Ba ya son kowane namiji ya raɓe ta hatta abokan sa, shi kaɗai kawai yake so ya kasance a rayuwar ta.

Matar ta bayyana yadda mijin ta yake kulle ta a cikin gida idan zai tafi wurin aiki duk domin kada wani namiji ya kwace masa ita saboda tsabar kishi. Ta daure ta cigaba da zama da shi duk da halin ƙuncin da take ciki na rayuwa tare da shi.

Bayan wasu shekaru sun haifi yara guda huɗu, inda ɗaya ya rasu, hakan ya bar su da yara uku. Wata rana ta nemi iznin da ya bart a ta fara sana’a domin taimakawa wajen ɗaukar dawainiyar gida, a mamakin ta ƴa amince

Ta samu aiki a matsayin ‘yar aikin gida a cikin birnin Nairobi na ƙasar Kenya, hakan ya sanya ta koma can da zama inda take kawo musu ziyara lokaci bayan lokaci.

Ya gargaɗe ni cewa idan na ci amanar sa sai ya kashe ni.

Sai dai a yayin da take can tana riƙe masa amana shi kuwa mijin na ta tuni har ya koma wurin wata matar. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bata ba, bayan ta dawo ta tarar da shi da wata mata.

Ta yanke shawarar komawa birnin Nairobi kawai, amma yaƙi yarda inda yayi mata barazanar zai kashe ta idan ta tafi.

Bayan ta koma Nairobi, ya kira ta a waya inda yayi barazanar kashe ‘ya’yan su idan har ba ta dawo ba. Dole ta sanya ta dawo inda su ka cigaba da zama da ɗayar matar wacce su ke samun saɓani sosai.

Bayan wani lokaci, ta yanke shawarar zuwa gidan da tayi aiki a Nairobi domin amso kuɗaɗen da take bin su bashi, amma mijin nata yayi tunanin guduwa za tayi ta bar shi. Sai ya tura wa ɗan’uwan ta sakon waya cewa zai kashe ta.

Kafin ɗan’uwan na ta ya sanar da ita, har ya kai mata farmaki da adda wace ɗayar matar ta kawo masa.

Omolo tace:

Ina ta roƙon sa da ya daina amma ina yaƙi ji. Ya yayyanke ni inda na faɗi a ƙasa. Na cigaba da roƙon sa kan ya yafe min kar ya kashe ni, amma sai ya ce komai zan faɗa sai ya kashe ni sannan ya tafi gidan kaso.

Ya cigaba da sarar ta inda ya yanke ta a hannun dama, bayan ta da ƙafaɗar ta da adda, sannan ya cire mata ido daga nan kawai sai ta daina motsi.

Yayi zaton cewa ta mutu, sai ya kyaleta yaje yasha guba domin ya mutu amma bai yi nasara ba, daga nan sai ya kai kan sa ofishin ‘yan sanda.

An garzaya da Omolo zuwa asibiti, cikin nasara ta rayu. Yanzu haka tana sayar da kayan marmari a bakin hanya domin samun abinda za ta kula da kanta da iyalin ta.

Ga bidiyon hirar da akayi da ita:

Yadda wani mai gona ya ƙwaƙule idon yaro ɗan shekara 16 a Bauchi

Wani yaro mai shekaru 16 a duniya, mai suna Uzairu Salisu, ya rasa idanun sa bayan wani da ya ɗauke shi aiki ya ƙwaƙule su a ƙauyen Dutsen Jira cikin yankin Yelwa, a jihar Bauchi, ranar Alhamis 23 ga watan Yuni, 2022.

Shafin LIB ya rahoto cewa, a wata sanarwa wacce kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Ahmed Mohammed Wakili, ya fitar, ya bayyana cewa mai garin ƙauyen ne ya kawo rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe