27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

China ta kirkiro wata nau’ra da take iya gano ko mutum ya kalli bidiyon batsa domin a rage yawan kallon bidiyon batsar 

IlimiChina ta kirkiro wata nau'ra da take iya gano ko mutum ya kalli bidiyon batsa domin a rage yawan kallon bidiyon batsar 

Kasar China ta kirkiro wata nau’ra, wadda ake yi mata lakabi da mai dani har hanji, wadda zata iya karanta tunanin mutum ta gano, ya kalli bidiyon batsa ko bai kalla ba, a kokarin da kasar take yi na haramta kallon duk wani abu da ya shafi tsiraici. 

Kwararrun masu bincike, na kasar China, sun yi ikirarin cewa sun kirkiro wata nau’ra mallakar hukuma, wadda “ zata iya  karanta tunanin mutum” kuma ta gano idan yana kallon bidiyon batsa. 

bidiyon batsa
bidiyon batsa

Ita wannan nau’ra, anyi ta ne yadda zata iya binciko wadansu jijiyoyi wadanda aikin su  yake farawa da zarar mutum ya fara kallon bidiyon tsiraici ko batsa. 

Yadda aka gwada mutane domin a gano masu kallon bidiyon batsa

An fara gwajin wannan nau’ra ne da wadansu maza yan makaranta su goma sha biyar 15, wadanda aka sanya su a gaban madubin kwamfiyuta suna kallon bidiyon batsar, yayin da kuma nau’rar tana daure a kawunan su. Daga nan kuma, ita nau’rar zata iya gano wa tare da zakulo duk wani hoto ko bidiyo koma dukkanin wani abu da ya shafi batsa, tayo nuna shi. 

Malamin Xu Jianjun, wanda shine ya gudanar da binciken, wanda kuma shine darakta a bangaren fasahar kere-keren lantarki, a jami’ar  Jiaotong ta Beijing, ya ce, dalilin kirkiro nau’rar shine domin  ta iya gano munanan bayanai, inda ya tabbatar da cewa kaso 80 cikin 100 na bayanan nau’rar gaskiya ne, sannan kuma zata iya gano wasu bayanan ma wadanda basu da alaka da batsa, idan aka aika mata da bayanan da ba na batsa ba. 

Kallon bidiyon batsa haramun ne a kasar China

Kasantuwar kallon batsa haramun ne a kasar China, jami’an gwamnati a kasar suna matukar tsaurarawa wajen binciko masu laifin ta hanyar hadakar aiki da wadansu cibiyoyi da suka sanyawa suna ” masu gwajin batsa ” wadanda aka baiwa aikin bincika yanar gizo domin zakulo bayanai da suka shafi batsa.

Mahaifin wata ‘yar TikTok ya kwanta dama bayan ganin bidiyonta tana rawar wakar batsa

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito bidiyon wani mutum yana bayani, ya ce wani malamin addini ne ya ga diyarsa tana rawar TikTok wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kamar yadda mutumin ya bayyana, daya daga cikin daliban malamin ya dade yana ganin diyarsa tana rawar amma sai yana kokwanton idan diyar malamin ce.

Ya ci gaba da shaida cewa watarana ya ga yarinyar ta saki wani bidiyo na rashin kyautawa, sai ya dauka ya nunawa mahaifinta bayan sun gama karatu.

Ya bayyana cewa an nuna masa bidiyoyi fiye da hamsin na diyarsa wadanda take nuna tsiraicinta da kuma rashin tarbiyya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe