24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda mata ta gane cewa mijinta mace ne bayan watanni 10 da auren su

LabaraiYadda mata ta gane cewa mijinta mace ne bayan watanni 10 da auren su

Wata mata ta gano cewa mijinta da su ka kwashe watanni 10 da aure mace ne, duk da sun kudanci juna ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kamar yadda Daily Mail ta bayyana.

Matar wacce ‘yar kasar Indonesia mai suna NA, mai shekaru 22 ta maka mijinta a kotu wanda likitan kwakwalwa ne bayan ya kammala karatu a New York.

Ma’auratan sun fara haduwa ne a yanar gizo, inda mijin sunansa Ahmaf Arrafif a garin Jambi.

Bayan fara soyayyar a yanar gizo sai su ka hadu a fili inda Ahnaf ya kai wa NA ziyara ya kwashe mako daya tare da duba iyayenta marasa lafiya.

Bayan mako daya da haduwa, iyayen NA sun sanya musu albarka inda su ka amince da batun auren, Tribune News ta ruwaito.

Bayan watanni hudu da aurensu, ‘yan uwan NA sun fara zargin mijin nata.

Ahnaf bai taba gabatar mata da iyayensa ba kuma sun ci gaba da shirye-shiryen auren yayin da ya sanar da ita shi cikakken likita ne.

Mahaifiyar NA ta yi mamakin yadda Ahnaf bai taba cire sutturarsa ba kuma ba ya wanka a idan da mutane a gidan.

Bayan matar ta fuskancesa sai ya bayyana mata cewa yana da kuraje a kirjinsa ne kuma wata matsala ce a jikinsa.

Daga bisani, mahaifiyarta ta bukaci ya tube sutturarsa gaban kowa don ya tabbatar musu da cewa shi namiji ne.

Daga nan ne Ahnaf ya bayyana cewa shi mace ne, sunansa Erayani kuma ya yi karya ne akan komai har da aikinsa.

NA ta sanar da kotun yankin Jambi cewa bata taba zargin mace ne mijin da ta aura ba har sai da mahaifiyarta ta fara zarginsa.

A cewarta, sun dade su na kusantar juna kuma a tsawon lokacin hannunsa yake mata amfani da shi.

Yanzu haka Erayani tana kotu akan karyar da ta yi akan cewa ita likita ne kuma namiji ce ita.

Matar aure ta halaka bokan da ya bata maganin kisa maimakon na mallakar mijinta

Wata matar aure ta halaka wani boka a Tudun Wadan Dan Kande da ke Jihar Kano bayan ta je neman taimako a wurinsa, Alfijir Hausa ta ruwaito.

Safiya ta garzaya wurin wani boka don neman taimako a wurinsa, ya bata maganin da zata zubawa mijinta ya kara sonta.

Sai dai bokan ya bukaci ta tafi bayan kwana biyu ta koma. Bayan ta koma ne ya bata maganin kuma ya sanar da ita yadda zata yi amfani da shi.

Bisa rahoton da AlfijirHausa ya bayyana, bayan ta yiwa mijinta amfani da maganin ya kwanta ciwo wanda daga nan ya sheka lahira.

Anan ne ta gano cewa maganin mutuwa bokan ya bata don ta sanya wa mijin kasancewar ya kamu da sonta.

Da ta koma yi masa korafi akan batun mutuwar mijinta, ya jajanta mata sannan ya tabbatar mata da cewa yana sonta kuma aurenta yake son yi.

Ya bukaci ta bashi dama ya aureta kamar yadda ta shaida, daga nan ta amince bayan kwanaki suka yi aure.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe