28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Fitowata daga gidan aure ya bani damar shiga fim, Maryam Shu’aibu (Junaidiyya)

LabaraiKannywoodFitowata daga gidan aure ya bani damar shiga fim, Maryam Shu’aibu (Junaidiyya)

Jaruma Maryam Shu’aibu ta fitaccen shirin nan mai dogon zango watao Gidan Badamasi, Junaidiyya ta bayyana cewa mutuwar aurenta ne ya bata damar shiga fim.

A wata tattaunawa da BBC Hausa a shirinsu na Daga Bakin Mai Ita su ka yi da ita, ta ce bata kashe aurenta musamman saboda tayi fim ba.

A cewarta, tun tana karama take da sha’awar shiga harkar, amma sai kuma tayi aure, bayan ta yi aure ta yi tunanin zata zauna har abada da mijinta sai kuma rabuwa tazo.

Ta bayyana cewa an haifeta Jos kuma ta girma a Jos, ta taba aure kuma tana da da.

Da aka tambayeta idan ta kashe aurenta ne musamman don ta yi fim, sai ta kada baki tace:

“Toh nidai gaskiya ban kashe aurena saboda in yi fim ba. Na yi aure ne ba wai da niyyar in fito ba, na yi aure ne dai kuma haka Allah ya kaddara cewa zan fito din.

“Kuma fitowana shi ne ya bani dama har na shiga fim. Don gaskiya da bana tunanin tunda na yi aure na cire fim a raina. So fitowar nan da nayi shi ne yasa ni har na shigo fim gaskiya.”

Ta ce tana da niyyar kara aure kwanan nan ba da jimawa ba. Kuma tana matukar jindadi idan ta gane mutane har ganeta suke yi.

Ta bayyana abu mafi bakin cikin da ya sameta shi ne rasa iyayenta duka biyu da tayi.

Abinda ya fi faranta mata rai shi ne idan ta tuna cewa tana da da. Ta kuma ce tana matukar bakin ciki idan ta ji mutane suna aibata ‘yan fim.

Dalilin da ya hana Adam Zango zuwa daurin auren Ummi Rahab

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna, manya-manya jarumai sun samu damar halartar daurin auren Lilin Baba da Ummi Rahab, amma banda Adam A. Zango.

Ali Nuhu shi ne wakilin ango inda ya amsar masa auren amaryarsa kuma bidiyon wurin daurin auren ya tabbatar da hakan.

Manyan jarumai maza sun yi nasarar zuwa wurin daurin auren inda su ka yi wa jaruman kara tun daga Ali Nuhu, Umar M Sherif, TY Shaban da sauransu.

Bayan kammala daurin auren an zarce wurin cin abinci wanda bisa bidiyon da ya bayyana, an bankare rago kowa na ta yanka yana sa albarka.

Mutane da dama sun yi mamakin rashin zuwan Adam A Zango kasancewarsa tsohon ubangidanta, sai dai ana tunanin ya yi hakan ne don zaman lafiya.

Ya yi gudun zuwa wurin wata tarzoma ta tashi daga wurin yaransa ko kuma habaici ko makamancin hakan, don haka kada ayi badi ba rai.

Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata rikici ya hautsine bayan ya cire jarumar daga shirinsa mai dogon zango, Farin Wata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe