24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda wani mai gona ya ƙwaƙule idon yaro ɗan shekara 16 a Bauchi

LabaraiYadda wani mai gona ya ƙwaƙule idon yaro ɗan shekara 16 a Bauchi

Wani yaro mai shekaru 16 a duniya, mai suna Uzairu Salisu, ya rasa idanun sa bayan wani da ya ɗauke shi aiki ya ƙwaƙule su a ƙauyen Dutsen Jira cikin yankin Yelwa, a jihar Bauchi, ranar Alhamis 23 ga watan Yuni, 2022.

‘Yan sanda sun yi ƙarin haske kan lamarin

Shafin LIB ya rahoto cewa, a wata sanarwa wacce kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Ahmed Mohammed Wakili, ya fitar, ya bayyana cewa mai garin ƙauyen ne ya kawo rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

62b568a9e4d9a
Yadda wani mai gona ya ƙwaƙule idon yaro ɗam shekara 16 a Bauchi. Hoto daga shafin LIB

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa sunan yaron Uzairu Salisu, wanda yake zaune a kwatas ɗin kwanan Gulmammu Jahun.

Yaron ya bayyana cewa wani mai suna Ibrahim mazaunin Rafin Zurmi, wanda ya sani na wani lokaci, ya ja shi zuwa daji domin yi masa aiki a gonar sa, wanda ake zargin Ibrahim yayi amfani da wayar kebur ya shaƙe shi sannan ya ƙwaƙule masa idanun sa guda biyu.

Yaron na amsar magani a asibiti

Wakili yace yaron yana asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) inda ake duba lafiyar sa yayin da ake ƙoƙarin cafke wanda ake zargin.

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona su ka jefa gawar maigidan su a rijiya bayan sun halaka shi a Abuja

A wani labari na daban kuma, wasu ma’aikatan gidan gona sun halaka maigidan su a Abuja. Ma’aikatan kuma sun jefa gawar sa a cikin rijiya bayan sun halaka shi. Mummunan lamarin dai ya auku ne a ƙaramar Kuje, ta birnin tarayya Abuja.

Yan sanda a Abuja sun bayyana yadda ma’aikatan gidan gonan wani manomi, Hussaini Aliyu Takuma, su ka halaka shi sannan su ka jefa gawar sa cikin wata rijiya kusa gonar sa a ƙauyen Jeida, cikin ƙaramar hukumar Kuje, a Abuja.

An jefa gawar sa cikin rijiya bayan an halaka shi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa manomin ya ɓace ne a gonar sa a ranar 2 ga watan Yuni, 2022, sai dai bayan gudanar da kwakkwaran bincike an samu cewa kashe shi akayi sannan aka jefa gawar sa cikin rijiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe