22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An cafke ‘yan ta’addan da su ka kai mummunan hari a cocin katolika ta Owo

LabaraiAn cafke 'yan ta'addan da su ka kai mummunan hari a cocin katolika ta Owo

Babban kwamandan hukumar tsaron Amotekun ta jihar Ondo, Chief Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa an kama wasu mutane da ake zargin su da kai hari kan masu ibada a cocin katolika ta St Francis, dake a Owo, cikin ƙaramar hukumar Owo ta jihar.

An kwato motoci da makaman da su kai hari da su a cocin

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Adeleye ya bayyana hakan ne a Akure, babban birnin jihar. Yace hukumar ta kuma gano wasu motoci da makaman da waɗanda ake zargin su kayi amfani da su.

A cewar sa:

Mun cafke da yawa daga cikin waɗanda su kayi ta’addanci a cocin katolika ta St Francis a Owo.

Mun kuma ƙwato motar da su kayi amfani da ita wurin kai mummunan harin. Sannan kuma mun ƙwato wasu daga cikin makaman su.

Sun zo a kan babura sannan su ka ƙwace mota ƙirar Golf.

Mun samu nasarar ƙwato motar sannan nan ba da dadewa ba za mu cafke dukkanin maharan.

Harin Owo: Tinubu, Da wasu gwamnoni sun ba da gudummawar Naira miliyan 125 ga wadanda harin Owo ya rutsa da su

A wani labari na daban kuma, Tinubu da wasu gwamnoni sum bayar da gudunmawar maƙudan kuɗaɗe ga mutanen da harin cocin Owo ya ritsa da su. Wasu mahara ne dai ɗauke da bindigogi su ka farwa cocin inda su ka halaka mutane da dama yayin da wasu kuma su ka jikkata ciki kuwa har da ƙananan yara.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa  kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Litinin, ya ziyarci garin Owo, inda ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe masu ibada da dama a wata cocin Katolika.

Irin haka bai taba faruwa ba

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo shi ne ya tarbi Mista Tinubu.
Da yake jawabi a fadar Olowo na Owo, Mista Akeredolu ya bayyana wannan Lahadi ranar da lamarin ya faru , a matsayin “bakar Lahadi.”

Ba a taba samun makamancin aika aika irin haka ba a Kudu maso Yamma,” in ji gwamnan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe