27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda wani mutum ya zane danfashi da makamin da yayi yunkurin ya wa matarsa fyade

LabaraiYadda wani mutum ya zane danfashi da makamin da yayi yunkurin ya wa matarsa fyade

Wani mutum ya lakadawa danfashi da makami bakin duka yayin da ta yi yunkurin yiwa matarsa fyade a Ondo, inda ya kwace bindigarsa, LIB ta ruwaito.

‘Yan sanda sun yi ram da Tosin Ominiyi bayan ya sace tsadaddun abubuwa a wani gida da ke Idanre, cikin karamar hukumar Idanre a jihar, sannan ya yi yunkurin yiwa wata mata fyade.

Yayin da Tosin da wasu mutane 13 suka bayyana gaban manema labarai ranar 22 ga watan Yuni, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami ya ce wanda ake zargin ya shiga gidan ne da misalin karfe 1 na dare ta taga.

A cewarsa, ta sace duk wani tsadadden abu a gidan sannan ya yi yunkurin yi wa matar gidan fyade wanda daga nan mijinta yayi kukan kura ya fada masa.

Bisa taimakon makwabta, sun kwace bindigar danfashin sannan suka zane masa jikinsa.

An kama mahaifiyar wanda ake zargin, Tale Akinlabi, mai shekaru 55, bisa taimakonsa da boye kayan satar. Kuma za a gurfanar dasu gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Ana zargin Omoniyi ya dade yana yiwa mutane da dama fashi a garin.

Mahaifiyarsa ta ce ta san dai danta dan acaba ne, amma ta yi mamaki da aka kama shi da fashi da makami.

Sauran masu laifin da aka kama sun hada da Jimph Dele, Ojo Rotimi, Uwanfor Destiny, Babajide Moses, Tope Gbenga, John Simon, Akinniranye Blessing, Jude Stephen da Iranlowo Ayomide.

Na gaji da cin bakin duka a hannun matata a raba mu, magidanci a gaban kotu

Wani manomi, Williams Famuyibo, a ranar Laraba ya bukaci wata kotun Mapo mai darajar farko da ke Ibadan da ta raba aurensa da matarsa mai cuzguna masa, Sola saboda tana yawan jibgarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Famuyibo, wanda ke zaune a Ibadan, ya ce a halin yanzu bazai cigaba da jure dukan da take nada masa ba.

“Na tsere daga gidana a watan Janairu.

“Ya mai girma mai shari’a, saboda irin hantarata da cin zarafina da Sola takeyi, a halin yanzu ina zama ne tare da ‘dan uwana.

“Maganar gaskiya, bana samun kwanciyar hankali saboda bata kula dani.

“Ina da ‘ya’ya biyar kafin in auri Sola a shekarar 1990, amma dukkansu na gurin ‘yan uwana saboda munayen halayen Sola,” a cewar Famuyibo.

Sai dai Sola bata halarci zaman kotun ba ko kuma ta turo da wakili duk da sammacin da aka kai ma ta.

Shugaban kotun, SM Akintayo, ya umarci mai bada sammaci da ya sanar da wacce ake kara ranar da za’a sake zaman kotu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe